Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 05.12.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 05.12.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 05.12.2018

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya dawo gida Ankara bayan halartar taron G20 da kuma kasashen Paraguay da Venezuela. A yayin taron manema labarai da Erdogan ya gudanar a filin tashi da saukar jiragen sama na Esenboga dake Ankara ya ce, za su ci gaba da karfafa alakarsu da kasashen Latin Amurka da Karibiyan.Shugaba Erdogan ya kuma ce, sun shirya murkushe duk wani nau'i na ta'addanci a kasar.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Shugaban Babbar Majalisar Dokoki ta Kasa ta Turkiyya (TBMM) Binali Yildirim ya bayyana cewa, Turkiyya babbar kawar China a bangaren nahiyar Asiya dake bangarenta. Yildirim ya ziyarci Babbar Birnin kasar China Beijing a wani bangare na ziyartar kasar da yake yi inda ya gana da Firaminista Li Kachiang a gidan saukar bakin gwamnati na Congnanhay. A yayin ganawar Yildirim ya ce "Muna magana ne kan kasa da take da muhimmanci a Asiya kuma a kan hanyar Silk Road da ake yi."

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Matar Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan da ta raka mijinta Rcep Tayyip Erdogan zuwa kasar Venezuela ta samu tarba na musamman daga matar Shugaban Kasar Nicolas Moduro mai suna Cilia Flores de Maduro. An kada waka ta kasa ta musamman da ake kira EL SISTEMA a Venezuela a yayin karrama Emine Erdogan. Yara da matasa ne suka yi kidan mai kayatarwa. A zaman na musamman an kada wakar A lokacinda nake zuwa Uskudar, Tare Muka yi tafiya da Amarya ruwan dorawa.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, za a kara yawan jiragen yaki marasa matuki da ake ba wa dakarun Turkiyya. Hukumar Kula da Masana'antun Tsaro ta Turkiyya na ci gada da karfafa yawan aiyukanta don samar da işsasshun kayan tsaro ga dakarun Turkiyya. A karkashin wannan manufar ana samar da jiragen yaki marasa matuki, kayan aiki da kuma manyan makamai na kassarawa tare da kashe 'yan ta'adda.

Babban labarin jaridar Star na cewa, fina-finan da Turkiyya ke samarwa sun samu karbuwa a kasar Labanan. Fina-finan sun samu karbuwa tun daga shekarar 2007 inda a yanzusuka maye gurbin fina-finan Masar, Siriya da Mekziko inda suka mayar da hankulansu kan na Turkiyya. Maza da dama dake Labanan na mayar da hankali wajen kallon fina-finan a manufarsu na koyon yaren Turkanci. Mata kuma suna son hikayoyi da fina-finan ban tausayi.Labarai masu alaka