Manyan labaran wasu jaridunTurkiyya 04.12.2018

Manyan labaran wasu jaridunTurkiyya 04.12.2018

Manyan labaran wasu jaridunTurkiyya 04.12.2018

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Turkiyya ta bayyana cewar a mako dayan da ya gabata ta kai farmakai daban-daban inda ta kassara 'Yan ta'adda 14 da suka hada da shugabanninsu 2. Rubutacciyar sanarwar da aka fitar ta ce, a farmakan da aka kai a fadin Turkiyya an kama masu alaka da 'yan ta'addar aware na PKK 598, masu alaka da 'yan ta'addar Fethullah (FETO) 538 sai masu alaka da 'yan ta'addar Daesh 17. Haka zalika sanarwar ta ce, an kuma kama masu alaka da 'yan ta'addar hagu su 10.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Hukumar Kididdiga ta Turkiyya (TUIK) ta bayyana cewar, hauhawar farashin kayayyaki a watan Nuwamba ya sauka da kaso 1.44. Hukumar ta ce, a tsawon shekara daya kuma hauhawar farashin a Turkiyya ya sauka da kaso 21.62. 

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Shugaban Sashen Sadarwa da Yada Labarai na Hukumar Masana'antun tsaro da Kayan Jiragen Sama ta Turkiyya (TUSAS) Tamer Ozmen ya bayyana cewa, nan da wani dan lokaci za su karbi lasisin da zai ba su izinin itar da jirgin sama mai saukar ungulu samfurin Atak zuwa Pakistan. Ozmen ya ce, ba gaskiya ba ne labarin da ake yadawa na cewar sakamakon matsalar karbar lasisin hakan zai janyi dage lokacin da aka shirya don mikawa Pakistan jiragen na yaki masu saukar ungulu. za a ci gaba da aikin kamar yadda aka tsara.

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, Tare da taimako da tallafin Ma'aikatar Raya Al'adu da Yawon Bude Ido ta Turkiyya za a nuna shirye-shiryen fim na Turkiyya da suka hada da "Diriliş Ertuğrul", "Payitaht: Abdülhamid", "Bir Zamanlar Çukurova"  "Çukur" a wajen taron ATF Asia TV Forum wanda za a gudanar a kasar Singapore inda  masu shirya fina-finai na duniya za su hadu da juna tare da masoyansu. A wajen baje-kolin za a gabatar da wata tattaunawa da ta kunshi kwararru inda za su duba masana'antar shirya fina-finai ta Turkiyya dake kai fina-finanta zuwa kasashen duniya sama da 150 tare da samun kudi da ya haura dala miliyan 150.

Babban labarin jaridar Star na cewa, Ma'aikatar Raya Al'adu da Yawon Bude Ido ta Turkiyya ta sake nade kafar wanda domin masu sana'ar wasan harbin da kwari da ba ka. Wannan mataki ya biyo bayan matakin sanya wasan "Dede Kurkut" na Turkiyya da Hukumar Cigaban Ilimi da Raya Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta yi a jerin kayan al'adu da ba za a iya taba su ba. Ma'aikatar ta Raya Al'adu da Yawon Bude Ido ta Turkiyya ta ce, za ta yi taro tare da tattaunawa wannan batu a taron KWamitinta da za a ta gudanar a shekarar 2019.Labarai masu alaka