Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 26.11.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 26.11.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 26.11.2018

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Masana'antun Tsaro na Turkiyya, a wannan shekarar bayan yarjejeniyar da suka kulla na fitar da MILGEM da jirgin yaki maisaukar ungulu na Atak, za su fita da karfi don halartar kasuwar baje-kolin kayan tsaro da za a yi a Pakistan. Za a gudanar da baje-kolin a tsakanin 27 da 30 ga watan Nuwamba a garin Karachi na Pakistan a karo na 10. Sunan baje-kolin "Baje-kolin kayan tsaro na kasa da kasa ta IDEAS" inda a wani bangare na kasuwar za a gabatar da tarukan karawa juna sani. Wakilan kasashen duniya da dama za su halarci taron.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, a karkashin manufar Hukumar Masana'antun Tsaron Turkiya na samarwa da dakarun kasar isassun makamai, an mika Kirpi 2 da kamfanin BMC ya samar. Kirp 2 na iya daukar makamai, kayan yaki da dakaru kalau. Zai iya taimakawa wajen daukar runduna tare da kare ta daga barazanar bama-bamai manya da kana na hannu.

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Taliya da Makaroni a Turkiyya Abdulkadir Kulahcioglu ya bayyana cewa Turkiyya na fitar da Taliya da Makaroni zuwa kasashen duniya 144. Ya ce, a shekarar 2016 sun fitar da tan dubu 831, a shekarar da ta gabata kuma sun fitar da tan miliyan 1 da dubu 55. A wannan shekarar suna hasashen za su fitar da tan miliyan 1 da dubu 200 zuwa waje. Ya ja hankali da cewar an fi fitar da taliya da makaronin zuwa kasashen Afirka wanda adadin da suke saya ya karu da kaso 68.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, kayan marmari na "Ejder" da aka gano a gundumar Gazipasa dake Antalya tare da gwada tabbatar da za a iya rayuwa da shi, ya zama abincin kasashe masu zafi da ya fito a Turkiyya wanda za a iya amfani da shi a abinciccika da dama.Labarai masu alaka