"Sai mun kwato Sham daga hannun PKK"

A ranar Jumma'ar nan da ta gabata,shugaba Erdoğan ya ce sai sun ceto arewacin Sham daga hannayen kungiyoyin ta'adda na YPG da na PKK, ko ta halin kaka.

"Sai mun kwato Sham daga hannun PKK"

A ranar Jumma'ar nan da ta gabata,shugaba Erdoğan ya ce sai sun ceto arewacin Sham daga hannayen kungiyoyin ta'adda na YPG da na PKK, ko ta halin kaka.

Shugaban na Turkiyya ya furta wadannan kalaman a albarkacin bikin karrama daliban makarantar jandarma da ta jami'an tsaro na gabobin teku,wanda aka shirya a Ankara, babban birnin kasar,inda ya ce:

"Kamar yadda muka ceci Afrin, sai mun kwato garuruwan arewacin Sham,wadanda suka hada da Manbij,Ain Al-Arab,Tel Abyad daga hannayen tsinannun kungiyoyin ta'adda masu zubda jinin bayin Allah da kuma yin da'awar raba kanun jama'a".

A ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2018, rundunar sojojin Turkiyya ta kaddamar da farkaman tsaro na reshen zaitun a yankin Afrin na arewa maso yammcin Najeriya,inda  ta cimma gaggarumar nasara a ranar 18 ga watan Maris na bana,bayan ta yi kaca-kaca da kungiyoyin ta'addar YPG,PKK da kuma DAESH.

Turkiyya wacce ta share shekaru 30 tana yakar PKK, Amurka da kuma Tarayyar Turai sun ayyana wadannan kungiyoyin a matsayin haramtattu.

PKK da reshenta da ke Sham,wato YPG,sun kashe sama da mutane dubu 40,000.


Tag: pkk , ypg

Labarai masu alaka