Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 12.09.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 12.09.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 12.09.2018

Babban labarin jaridar Star na cewa, Kakakin Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalin a lokacin da ake ci gaba da gudanar da taron Majalisar Ministoci a Kulliyar Bestepe ya yi kira da kawo karshen hare-hare da ake kai wa Idlib inda ya nuna bukatar da ke akwai na a tsaya a madogara ta siyasa don warware rikicin. Ya ce, kai hare-hare Idlib za kawo cikas ga yunkurin amfani da siyasa don warware rikicin Siriya. Ya ci gaba da cewar kiran da za su yi shi ne, AMurka da dukkan kasashen gabas ta tsakiya da na Turai su hada kai a siytasance don kawo karshen wannan rikici.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, a taron Ministocin Harkokin Wajen Turkiyya-Romaniya-Polan da aka yi a Romaniya, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya ja hankali kan cewar rikicin Siriya ya shafi kowa da kowa, kuma suna aiyuka da kasashen da suke da ra'ayi iri daya da su. Cavusoglu ya ce, gwamnatin Siriya da Rasha na ci gaba da kai wa Idlib hare-hare kuma bukatarsu a bayyana ta ke "A dakatar da kai wa Idlib hari." Ya kamata a yi aiki tare don yaki da ta'addanci.

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya Hami Aksoy ya ce "Rufe Ofishin Kungiyar 'Yantar da Falasdinawa (FKO) na nuna yadda Amurka ta dauki bangare a rikicin Gabas ta Tsakiya." Aksoy ya ce, za su ci gaba da zama tare da Falasdinawa a gwagwarmayar neman hakkinsu da suke yi.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, a gundumar Ceylanpinar da ke lardin Sanliurfa na Turkiyya kuma ta ke iyakar kasar da Siriya an kafa tutar Turkiyya maitsayim mita 150. An gudanar da biki a unguwar Ozbek wanda gwamnatin gundumar Ceylanpinar ta shirya. Mutane da dama da suka hada da Shugaban gundumar Ceylanpinar Menderes Atilla da shugaban AKP na gundumar Halid Simsek ne suka halarci bikin.Labarai masu alaka