Turkiyya ta jinjina wa Paraguay kan Qudus

Turkiyya ta jinjina wa Paraguay, sakamakon sauya tunani da ta yi game da matakin da ta dauka a baya na dage ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa tsarkakken birnin Qudus.

Turkiyya ta jinjina wa Paraguay kan Qudus

Turkiyya ta jinjina wa Paraguay, sakamakon sauya tunani da ta yi game da matakin da ta dauka a baya na dage ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa tsarkakken birnin Qudus.

Ministan harkokin wajen Paraguay,Luis Alberto Catiglioni ne ya fitar da wata sanarwa,inda ya ce, sun yi watsi da matakinsu na goya wa kasashen da ke yunkurin rura wutar fitina a Qudus baya.Saboda “Paraguay na son taka muhimmiyar rawa wajen samar da dauwamammiyar zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar amfani da diflomasiyya”.

Jim kadan bayan wannan sanarwar, Isra’ila ta maida martani,inda ta tabbatar da cewa za ta rufe ofishin jakadancin Paraguay da ke kasarta.

Haka zalika, tuni Amurka ta fara gasa wa shugabannin Paraguay aya a hannu da zummar tirsasa su sauya tunani.

Ministan harkokin kasar Turkiyya,Mevlüt Çavuşoğlu ya gana da takwaransa na Paraguay, Castiglioni ta wayar tarko,inda ya gode masa kan matakin da kasarsa ta dauka. 

A ranar 21 ga watan Mayun da ya gabata ne, kasar Paraguay ta dage ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa Qudus don mara wa shugaban Amurka, Donald Trump baya. Abinda yasa ta kasance kasa ta biyu bayan Guatemala,wacce ta yi maraba da wannan gurguwar shawarar.
 Labarai masu alaka