Gimbiyar Japan na gaf zuwa Turkiyya

Gimbiyar masarautar Japan,Akiko Mikasa za ta ziyarci biranen Ankara,Kırşehir da na Santambul daga ranar 9 zuwa 14 ga watan Satumban bana.

Gimbiyar Japan na gaf zuwa Turkiyya

Gimbiyar masarautar Japan,Akiko Mikasa za ta ziyarci biranen Ankara,Kırşehir da na Santambul daga ranar 9 zuwa 14 ga watan Satumban bana.

Ofishin jakadancin Japan da ke Ankara,babban birnin kasar Turkiyya,ne ya sanar da zuwan gimbiyar,inda aka ce za ta halarci wani bikin nuna kayayyakin tarihi da za yi gidan ajje kayan tarihi na Sakıp Sabancı na jami’ar Sabanci.

Bayan ta ziyarci kushewar tsohon shugaban kasar Turkiyya,marigayi Mustafa Kemal Atatürk da ke Ankara,gimbiya Akiko za ta yada zango gidan tarihin Kale-höyük da ke birnin Kırşehir.

A shekarar 2014 ma, Akiko ta kai kawo ziyara kasar Turkiyya.Labarai masu alaka