Erdogan: Amurka na biyan 'yan ta'adar FETO dala miliyan 850 a kowacce shekara

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewar Amurka na biyar 'yan ta'addar Fethullan FETO kudi har dala miliyan 800 zuwa 850 a kowacce shekara.

Shugaba Erdogan bayan gana wa da Shugaban Kasar Benin Patrice Talon da ya ziyarci Ankara sun gudanar da taron manema labarai.

Shugaba Erdoga ya ce, ya samu damar yin tattaunawa mai kyau kan 'yan ta'addar FETO.

Ya ce "Kamar yadda aka sani FETO ta zama wata annoba, ta shiga ko ina tare da haifar da matsaloli. Wakilan Asusun Ma'arif sun fara aikinsu a Benin a makon da ya gabata. Fatanmu shi ne mu samu sakamako mai kyau a kasar Benin game da 'yan ta'addar FETO."

Shugaba ya ci gaba da cewar kamar yadda FETO suka shiga ko'ina a Turkiyya, haka ma a Benin, za su iya shiga sauran bangarori.Labarai masu alaka