Shugaba Erdoğan ya taya Muktada As-Sadr murna

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya taya  jogaran gambizar jam'iyyun siyasa ta "Sairun",Muktada As-Sadr wanda ya lashe zaben kasar Iraki,murna.

Shugaba Erdoğan ya taya Muktada As-Sadr murna

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya taya  jogaran gambizar jam'iyyun siyasa ta "Sairun",Muktada As-Sadr wanda ya lashe zaben kasar Iraki,murna.

A ganawar da suka yi ta wayar tarho a jiya da yamma,shugaba Erdoğan ya ce yana fatan zaben da aka a ranar 12 ga watan Mayun bana a Iraki, tun bayan ganin bayan kungiyar ta'adda ta DAESH, ya zama alheri ga daukacin al'umar kasar.

Shugaban na Turkiyya wanda yayi tunatarwa game da muhimmanci hadin kai da zama tare cikin kwanciyar hankali da lumana, yayi fatan nasara ga Muktadar As-Sadr a aniyarsa ta gaggauta kafa gwamnati bayan zabe.

Erdoğan ya ce,an samu wasu mishkiloli a zaben na Iran a yankin Turkmen na Kerkuk,wadanda suka ce an mayar da su saniyoyi ware,shi yasa a shirye yake ya tallafa wa Muktada wajen gano wadannan matsalolin tare magance su.

Muktada As-Sadr yayi wa shugaba Erdoğan alkwarin zai kara hakkokin kabilun Turkmen da na illahirin al'umomin Iraki.

Shugaba na Turkiyya da jagoran "Sairun" ,sun jaddada aniyarsu ta karfafa dangantakar da tsakanin Turkiyya da Iraki.Labarai masu alaka