Manyan Labarai Daga Wasu Jaridun Kasar Turkiyya

Manyan Labarai Daga Wasu Jaridun Kasar Turkiyya

Manyan Labarai Daga Wasu Jaridun Kasar Turkiyya

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, Turkiyya na ci gaba da shiga tsakanin Amurka da Rasha, wadanda ke ci gaba da yakin cacar baki, tun bayan hari da makami mai guba da aka kai a yankin Duma na kasar Sham.A tsawon kwanaki 3, shugaba Erdoğan ya gana da takwarorinsa na Rasha da Amurka ta wayar tarho babu kakkautawa.Turkiyya wacce duniya ke ci gaba da kwakwanton matsayinta a wannan rikicin, ta bayyana aniyar ta kin ta goya wa kowa baya,inda a yanzu haka zage damtse don yayyafa ruwa a wutar wannan rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen 2.

Babban labarin Vatan na cewa,makaman da Turkiyya ta kera da karan kanta na ci gaba da nuna ingancinsu a hare-haren yakar ta’addanci.Masanan Turkiyya sun yi nasarar kera kyamarorin da ke gani cikin hayaki da wuwraren da haske ya dusashe.Tare wadannan  kere-keren za a tarwatsa duk wasu tarkokin da ‘yan ta’adda maha’inta suka haka. Wadannan na’urorin ,na kunshe da kwakwalen kwamfuta masu matukar aiki.Shi yasa suka fi na sauran sassan duniya da kadan.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, shugaban kungiyar masu aikin otel na kasar Turkiyya (TÜROB) ,Timur Bayandir, ya bayyana cewa a shekarar 2018, yawan masu yawon shakatawan da zasu zo daga Rasha zuwa Turkiyya, zai karu da kashi 20 cikin dari.A cewar bayanin da aka yi daga TÜROB,kafin gabatowar lokacin yawon bude ido, an rubuta wani rahoto kan bukatun masu yawon kashe kwarkwatan idanu na Rasha.Bayandir wanda ya tunatar da cewa, idan aka yi la’akari da da alkalumman bara,yawan masu yawon bude ido na Rasha wadanda suka kama dakuna a wata na farko na shekarar bana,a kamfanin TUI ya karu da kashi 1.5, a Tez Tour da Pegas ya ninka sau 2,a Intourisyt kuma ya ninka da kashi 5,6.Kazalika ya ce duba da alkalumman Skyscanner sun una cewa,duba bukace-bukacen siyan tikitin jirgin sama da aka samu gabanin gabatowar lokaci yawon bude ido, tsakanin 30 ga watan Afrilun da 9 ga watan Maytis na bana,a yanzy hakayawan masu yawon shakatawa sun karu da kashi 102 cikin dari.

Babban labarin Star na cewa,yau ne daren Israh wal Miraj na shekarar 2018 wanda Musulmai suka dade suna tsumaye.A wannan daren wacce a cikinta ne Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya gana da ubangiji a Sararin samaniya, za a bude hannayen zuwa sama don ninka addu’o’i.A tashin farko, Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yi tafiya daga Masallacin masjidul Haram zuwa Baitul muakddis “Aksa”.A tashi na biyu kuma daga Baitul mukaddis zuwa sama.Ana kiran wannan tafiyar da suna a”Isra”.Labarai masu alaka