Manyan Labarai Daga Wasu Jaridun Kasar Turkiyya

Manyan Labarai Daga Wasu Jaridun Kasar Turkiyya

Manyan Labarai Daga Wasu Jaridun Kasar Turkiyya

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa,Shugaban kasar Turkiyya Reccep Tayyip Erdoğan ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Ankela Merkel ta wayar tarho jiya da yamma, inda suka tattauna batutuwan da suka danganci alakar kasashen 2 da kuma matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya.Shugaban na Turkiyya ya yi amfani da wannan damar don yi wa Merkel da sabuwar gwamnatinta wacce ta sake dawowa kan karagar mulki, fatan Allah alheri.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, kungiyar hada kan kwastomomin kasar Saiparas ta Arewa ta bai shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan lambar yabo ta "Gwarzon shekarar 2018", a albarkacin wani biki na musamman da aka shirya a zauren Atatürk da ke Nicosia babban birnin kasar.Hak zalika, an bada lambobin yabon "Fittatun ma'aikatan shekarar 2018" da na "Fitattun jaridodin shekarar 2018" ga wadanda suka yi bajinta a bana.

Babban labarin jaridar Haber Türk na cewa, a wani jawabin da ya yi a albarkacin wani babban taro karo 6 da aka gudanar a Baku, babban birnin Azabaijan , Firaministan kasar Turkiyya, Binali Yıldırm ya tabbatar da cewa, Majalisar Dinkin Duniya ba ta warware mastalolin duniya,inda ya ce :

"Ba mu bukatar Majalisar Dinkin Duniya wacce za ta zama tamkar fagen goyayyar kasashe.Bukatar mu a yau ita ce Majalisar Dinkin duniya wacce za ta tsaya kan kafafunta don warware matsalolin duniya.Duniya na ci gaba tarwatsewa, amma maimakon dinke duniya, majalisar duniyar na zuba ido tana kwallo.A gefe daya mutane na mutuwa,ana amfani makamai masu guba don yi wa bayin Allah kisan kiyashi, amma kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, sabili da gogayyar da ke tsakanin kasahen duniya,ya kasa cewa uffan,ya kasa tabuka komai game da wadannan kazaman lamurran".

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, a wata ganawa da shugabannin kasashen Turkiyya ya yi da takwarot-rinsa na Azabaijan,Georgia da Iran a Baku, babban birnin kasar Azabaijan, kasashen 4 sun yanke shewarar hade layin dogon da ke tsakanin Reşt (Iran) da Astara (Azabaijan) da na Baku (Azabaijan) zuwa Kars (Turkiyya) wanda yake wucewa ta Tiflis (Georgia).Za a dai fara wannan aikin daga yankunan Çabalar da Bandar-Abbas na Iran.Manufar wannan gaggarumin aikin ita ce, gina wata katafariyar hanyar kasuwanci wacce  za ta hada  yankin tekun India da naTurai.

 Labarai masu alaka