Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyanawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson abubuwan da suka sanya a gaba game da Siriya da Iraki. A yayin ziyarar an tattauna batutuwan da suka shafi alakar kasashen 2 da kuma yankunansu baki daya.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Firaministan Turkiyya Binal, Yildirim ya tattauna da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin. Bayan ganawar da suka yi, shugabannin 2 sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa. Firaminista Yildirim ya ce, alakar Turkiyya da Jamus ta bude sabon shafi. Kuma a matsayinsu na shugabannin kasashen ba su ware lokaci yadda ya kamata don tattauana wa ba. Wannan abu ne da ya wuce. An shiga sabon lokaci. 

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Ministan Tsaron Turkiyya Nurettin Canikli ya gana da takwaransa na Amurka Jim Mattis a yayin taron NATO a birnin Brussels na kasar Beljiyom. Canikli ya fada wa Mattis cewa, za su iya yakar 'yan ta'addar PKK.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Babban Bankin Turkiyya ya bayyana cewa, a shekarar 2017 daga kasashen waje an zuba jari kai tsaye a kasar na dalar Amurka biliyan 7 da miliyan 437 inda Spaniya ce ke kan gaba wajen kara yawan zuba jarin. Kasar Holan kuma ita ce ta fi kowacce zuba jari a Turkiyya. Alkaluman sun ce, kasashen Turai sun zuba jari a Turkiyya na dala biliyan 4 da miliyan 964 a shekarar 2017.

 Labarai masu alaka