Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hürriyet cewa,mai magana da yawun shugaban kasar Turkiyya,Ibrahim Kalın ya gana da mai bada shawara kan tsaro na kasar Amurka, Laftanar Janar  McMaster a birnin Santambul.A ganawar, sun tabo batun tabbatar da ingantacciyar hulda tsakanin kasashensu 2 da kuma gano inda yake yi wa kasashensu kaikayi.Haka zalika,McMaster yayi musayar yawu  da Kalın na Turkiyya, wacce wata abokiyar ittafiki ce ta musamman,dangane dabaru da kuma tsare-tsaren dakile matsalolin da suka addabi Gabas ta Tsakiya.

Babban labarin Habertürk na cewa,shugaban Rundunar Sojin Turkiyya Janar Hulusi Akar yayi muhimmin jawabi kan Hare-haren “Reshen Zaitun”,inda ya ce : “daidai da digo daya na jinin shahidai da na tsaffin sojojin Turkiyya ba zai zama a kasa ba.Akar wanda ya halarci bincike da kuma atisayen da aka gudanar a yankin Hatay na kasar Turkiyya, ya ce babbar manufar da suka sa gaba game da hare-haren “Reshen Zaitun” ita ce tabbatar da tsaro, ‘yanci, zaman lafiya,kwanciyar hankali da lumana a Afrin tare da ceto yankin daga hannun haramtattun kungiyoyin ta’adda da kuma bai wa ‘yan Siriya da ke Turkiyya damar komawa kasarsu salim-alim.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, za a fara aiyukan da suka jibanci gina ma’adanin iskar gas a tafkin Tuz na kasar Turkiyya.Wannan ma’adinin wanda zai kasance a gundumar Sultanhanı zai cimma matakin biyan bukatun jama’an Turkiyya dari bisa dari a shekarar 2023.Ma’adinin iskar gas na tafkin Tuz, zai kunshi kashi 50 a cikin dari na bukatun makamashi na Turkawa, wanda ya daidai da mitakub biliyan 5,4.Haka zalika za’a dinka amfani da shi a duk lokacin da ake bukatar sa.

Babban labarin jaridar Star na cewa,ministan sadarwa,sufuri da na ayyukan da suka jibanci tekunan Tukiyya, Ahmet Arslan ya yi wa ‘yan kasarsa albishir  game kammaluwar ginin sabon filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Santambul da kashi 80 a ciki dari.Arslan ya ce a ranar 29 ga watan Oktoban shekarar bana, za a kaddamar da bikin bude kofofin wannan tashar jiragen saman,inda ya ce : “Zamu kaura a cikin awanni 48, mu kuma fara tayar da jirage sama a wannan filin a cikin sa’o’i 24”.

 Labarai masu alaka