Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a yayin ziyarar da ya kai Roma kafin gana wa Papa Franciscus ya gana da shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella. Bayan shekaru 59 Erdoğan ne shugaba na farko daga Turkiyya da ya ziyarci Vatican. A yayin ganawar ta Erdoğan da Papa za a mayar da hankali kan batu Kudus, matsalolin yankin, rikicin dan adam a Siriya, yaki da ta'addanci da kyamar Musulunci. 

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Firaministan Turkiyya Binali Yildirim ya bayyana cewa tun bayan fara kai hare-haren Reshen Zaitun a yankin Afrin an harba jimillar makaman roka zuwa Turkiyya 94 daga Siriya, 60 zuwa Hatay sai 34 da aka harba Kilis, inda kuma fararen hula 7 suka mutu, wasu 113 suka sami raunuka. A bayanin da Yildirim ya yi bayan ziyartar ofishin gwamnan Kilis ya ce, hare-hare da aka fara a ranar 20 ga watan Janairu na ci gaba da tafiya yadda ya kamata, kuma dakarun Turkiyya sun lalata mafakar 'yan ta'adda 538 tare da kashe 'yan ta'addar 935.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, Kakakin gwamnatin Turkiyya Bekir Bozdağ ya bayyana cewa, waje na 3 da Turkiyya za ta shiga don tsaftace shi daga 'yan ta'adda shi ne Munbic. Ya ce, idan sojojin Amurka za su saka kayan 'yan ta'adda su yawo a tsakaninsu to babu batun wariya da sojojin Turkiyya za su nuna yayin kakkabar da su.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, an samu karuwar kaso 13 cikin 100 wajen samar da injinan motoci a Turkiyya a shekarar 2017 idan aka kwatanta da 2016. A shekarar 2017 an samar da motoci kanana guda miliyan 1 da dubu 474. Samar da motocin kansu kuma ya karu da kaso 18 cikin 100 a 2017 inda aka samar da guda miliyan 1 da dubu 121.Labarai masu alaka