Farmakan Tafkin Zaman Lafiya

Manufar ita ce zaman lafiya,
ta'addanci ake nufa

Manyan Labarai Daga Wasu Jaridun Kasar Turkiyya

Manyan Labarai Daga Wasu Jaridun Kasar Turkiyya

Manyan Labarai Daga Wasu Jaridun Kasar Turkiyya

Babban labarin Sabah na cewa,a albarkacin wata liyafar da aka shirya a Seoul babban birnin Koriya ta Kudu,don martaba wakilan duniyar kwadago,firmanistan kasar Turkiyya Binali Yıldırım, ya tunatar da jama'a cewa Turkiyya da Koriya ta Kudu na murnar ci gaba da huldar diflomasiyya a tsakanin su a tsawon shekaru 60,inda ya ce :“Ina fatan a nan gaba,alakar da ke tsakaninmu ta haura matsayin huldar soja da samar da dabarun tsaro na bai daya.Ta hakan ne zamu cimma burin da muka sa a gaba na samar da aiyukan cigaba, da zummar kyautata makomar al’umomin kasashensu domin su rayu a cikin walwala da kuma yalwa.Abin farin ciki ne ganin yadda kamfanonin Koriya ta Kudu ke ci gaba da zuwa Turkiyya,wasunsu su kaddamar da aiyukan bai daya a tsakanin Koriya da Turkiyya,ga wadanda kawo yanzu ke ci gaba da shakku,ina so in tabbatar musu da cewa, Turkiyya na gabatar musu da dama marar misaltuwa a wajen habbaka kasuwancinsu”.

Babban labarin jaridar Star na cewa,Shugaban hukumar fitar da hajoji zuwa kasashen waje na tekun bahar Rum,Mahmut Arslan ya ce, idan aka yi la’akari da alkalumman shekarar bara, a watanni 11 na shekarar 2017, fitar da kayayyaki ya habbaka da kashi 18,4 a cikin dari, abinda ya yi daidai da dalar Amurka biliyan 10 da milyan 640.A wata rubutacciyar sanarwar da ya fita,Arslan ya ce, fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje na dada karuwa a kowace shekara,abinda yasa suke kara samun karfin gwiwar cewa, a shekarar 2018 zasu samu ci gaba haikan.

Babban labarin jaridar Hürriyet na cewa,Kamfanin duniyar kofi na kasar Turkiyya wanda aka bude a a shekarar 2004 ta karkata akalar harkokinta zuwa kasashen China da kuma Amuka,inda a shekara mai zuwa take sa ran bude shaguna 50 zuwa 100 a Sin.Shugaban kamfanin, Kaan Altınkılıç ne ya bayyana hakan,inda ya ce :”Mun yanke shawarar kara yawan kwastominmu ta hanyar sayar da kofinmu a duniya.Abinda yasa muke goyon bayan safarar sa zuwa kasashen waje”.

Babban labarin jaridar Haber Türk na cewa, A yayin da aka samu karuwar yawan masu yawon bude da kashi 60 a cikin dari a watanni 10 na farko shekarar bana a yankin Antaliyan kasar Turkiyya, wacce ta kasance cibiyar “Yawon bude ido ta duniya” kana garin da ya fi samun maziyarta a duk fadin duniya,sai a watan Nuwamban shekarar bana, alkalumman suka yi tashi gwauron zabo kamar a lokutan baya,inda aka samu karuwar yawan masu yawon bude ido da 1 a cikin dari,abinda yayi daidai mutane dubu 141.A jimillance a shekarar bana yawan masu yawon bude ido ya karu da kashi 58 a cikin dari, wanda yayi daidai mutane milyan 9 da dubu 617.An samo wadannan alkalumman ne daga cibiyar tashar jiragen sama ta yankin Antaliya.

 Labarai masu alaka