Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 23.11.2017

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 23.11.2017

853280
Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 23.11.2017

Babban labarin jaridar Hürriyet na cewa shugaban ƙasar Turkiyya ya bayyana cewar yarjejeniyar da aka gudanar a Shoci dake Rasha na samar da zaman lafiya a ƙasar da hanyar siyasa ba zata yi aiki akan ƴan ta'adda PKK/YPD ba. Waɗannan kungiyoyi dake kokarin rabuwar ƙasashe baza ayi masu sassauci ba.

Babban labarin Yeni Şafak na cewa Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewar duniyar Musulmi ta fara kuɓuta daga fitinan da ta samu kanta a ciki, lnda ya ƙara da cewar ƙasashen yamma na ƙoƙarin daƙile haddin kan ƙasashen Musulmi tare da dakile tattalin arzikin su da ci gaban su. Yayi wannan jawabi ne a taron ƙolin Majalisar Kasashen Musulmi , da hukumar tattalin arzikin kasashen musulmi karo na 33 

Babban labarin jaridar Vatan na cewa shugaban ma'aikatan wasikun Turkiyyar ( PTT) Kenan Bozgeyik ya bayyana cewar daga shekarar 2018 za'a samar da drone (wani nau'in mutum mutumi) da zai rinka raba wasiƙu a ƙasar. Wannan tsari injiniyoyi dake wasu jami'o'i kasar ke gudanar da aiki akansa.

Babban labarin Sabah na cewa ministan tsaron Turkiyya  Nurettin Canikli ya bayyana cewar Turkiyya zata karbi makami mai linzami sanfarin S-400 da zata saye daga hannun Rasha a 2019. Yayi wannan jawabi ne a lokacin da ya bayyana a gaban majalisar dokokin kasar.

Babban labarin jaridar Star na cewa Burhan Akbukad ya lashe gasar damben duniya da aka gudanar a Poland na ƴan ƙasa da shekaru 23 . Akbukad mai nauyin kilo 80 ya doke abokin hamayyarsa Lasha Gobadze daci biyu da ɗaya, Inda Turkiyya tazo na uku da samun medal guda hudu bayan jojiya da Rasha.Labarai masu alaka