Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Star na cewa, mai magana da yawun shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalın ya yi jawabi a gidan talabijan inda ya yi raddi da maganar da wakilin Amurka a yaki da ta’addan ci Brett McGurk ya yi na cewa Turkiyya tana da alaka da ‘yan ta’addan birnin Idlib. Kalın ya ce, ‘’wannan magana da ta fito daga Middle East Institute magana ce da ba za mu taba yarda da ita ba.’’

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, gobe za a yi babban taron rundunar sojojin Turkiyya a fadar Çankaya inda firaminista Binalı Yıldırım zai jagoranci taron. A taron ne za a tattauna kan lokacin ritayar manyan sojoji kamar su Janar da Kanar inda kuma za a yi jawabi game hanyoyin da sojoji za su bi domin cigaba a rundunar. Bayan an kammala taron ne shugaban kasar Recep Tayyip Erdoğan zai zartar da al’amarin karshe inda kuma za a bayyana sakamakon a jaridar gwamnati. Bayan yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli ne dai aka yanke shawarar yin gyra a rundunar sojojin.

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Turkiyya tana cigana da kusantar burin ta na shekarar 2023 dukda hare-haren da ‘yan kasar waje ke mata. Cigaban da Turkiyya ta yi a watanni 4 na farkon shekarar 2017 ya kai kaso 5 cikin dari inda da yin haka ta ninka adadin cigaban da sauran kasashen Turai suka yi. Kungiyar binciken Turkiyya ta TÜİK ta bayyana cewa makin da Turkiyya ta samu a kasuwar duniya cikin shekaru 3 da rabi ya fi na kowanne shekara yawa. ‘Yan kasashen waje sun zuba hannayen jari mai darajar Dala biliyan 2.1 tsakanin ranar 14 zuwa ranar 21 ga watan Yuli.

Babban labarin jaridar Habertürk na cewa, ‘yar kasar Turkiyya mai shekara 12 ta zo ta biyu a gasar ‘’International Ischia Piano’’ da aka yi a kasar Italiya. Nehir Özzengi ta kasance ta buga piyano na tsawon awa biyu a kowacce rana. Özzengi ta ce burin ta shi ne ta zagaya duniya inda za ta tallata wakar ta ta kuma tattalata al’adun kasar ta.Labarai masu alaka