Takaitatan labarai daga wasu manyan jaridun Turkiyya 19.07.2017

Takaitatan labarai daga wasu manyan jaridun Turkiyya 19.07.2017

Takaitatan labarai daga wasu manyan jaridun Turkiyya 19.07.2017

 

Takaitatan labarai daga wasu manyan jaridun Turkiyya 19.07.2017

Babban jaridar Sabah na cewa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, zai ziyarci kasashen gulf da miyyar samar da mafita ga rikicin da kasashen ke fama dashi da kasar Qatar. Ziyarar da zaiyi a ranakun 23-24 ga watan Yuli zai fara ne da kasar Saudiyya , Kuwait da Qatar. Zai gana da sarki Saudiyya Selman bin Abdulaziz, a inda zai nemi Saudiyya ta zama jagorar warware rikicin. Daga bisani ya zagaya zuwa Kuwait inda zai nemi kasar ta zama mataimakiyya ga Saudiyya don kawo karshen rikicin a inda zai gana da sarkin Kuwait  Sheyh Sabah Ahmel el Sabah. Daga karshe zai ziyarci Qatar a inda zai gana da sarkin Qatar Sheik Temim bin Hamed Al Sani.

Firaministan Turkiyya Bınalı Yildirim ya godawa ministan harkokin wajen Estonia Mikser akan goyon bayan da Estonian take baiwa Turkiyya a kokarint a na zama cikkakiyar mamban Nahiyar Turai. A lokacin da Yıldırım ya karbi bakawancin Mikser da tawagansa ya bayyana cewa yunkurin Turkiyya akan zama mamban Nahiyar nada muhinmanci sosai ta fannin tsaro. Tawagar Mikser sunyi alkawarişn cewa kasar Estonia zata ci gaba da goyawa Turkiyya baya akan manufarta ta zama cikkakiyar mambar Nahiyar Turan.

Babban jaridar Habertürk na cewa ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu,ya gana da manema labarai bayan ya gana da takwaranasa na Estonia Sven Mikser inda ya amsa tambaya akan matsalar Cyprus. “ Matsalar Cyprus dai ta zama kalubale a gabanmu, a yanzu dai wadanda basa son a warware matsalan tun daga taron Crans-Monstana sun bayyanan, masu son a waraware matsalar ma sun bayyana. Majalisar Dinkin Duniya da Nahiyar Turai ma sun farga da hakan. Çavuşoğlu ya bayana cewa Cyprus ta yamma dake karkashin Rum na neman ta rinki gudanar da aiyukan hidrokabon na yankin ita tilo, wannan ba dai-dai bane, saboda a wannan tsibirin akwai hakkin ‘yan arewacin Cyprus Turkawa.

Babban jaridar Hüriyet na cewa za a fara Wasan Bale na kasa da kasa a ranar 24 ga watan Yuli a Ankara. A wasan dai ‘yan rawa wararru zasu samu halarta daga kasashen Kuba, Spain, Kazagistan da Rasha.

Babban jaridar Yeni Şafak na cewa Hukumar Kare Yanayi kasar Turkiyya ta kara daukar wasu matakan kare ciyayi a kasar. A inda kuma ta samar da wata sabuwar tsiro mai suna “Yar Oktoba” Ministan ruwa da gandun dajin kasar Turkiyya Veysel Eroğlu ya bayyana cewa aikin mu shine mu kare wadanan tsiro mu kuma sarafa su ta yadda zasu anfane mu a nan gaba.

 

 Labarai masu alaka