Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa, abin takaici ne a ce kasar Rasha ta hada kai da 'yan ta'addar YPG/PYD da ke Siriya. Kuma kamar yadda na shaida musu dole ne a fatattaki wadannan 'yan ta'adda daga Siriya. Idan ba a kore su daga Siriya ba to aiyukan Turkiyya a kasar ba za su kare ba. Suna son kafa wata kasa. Babu siyasa irin wannan a duniya. Ya ce, Turkiyya ce ta fi damuwa da wannan abu.Tana da iyaka mai nisa kilomita 911 da Siriya. Idan Daesh ta harba makami ana kashe Baturke. A wajen su wadannan kasashe akwai abu irin haka? babu sam. Kar wani ya cewa Turkiyya wai ta bar kasar Siriya,hakan ba mai yiwuwa ba ne.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, an gayyaci mataimakin jakadan Rasha da ke Turkiyya sakamakon harba wni makami daga Afri a Siriya tare da kashe sojan Turkiyya 1. Kakakin ma'aikatar Huseyin Müftüoğlu an shaida wa mataimakin jakadan irin takaicin wannan abu da ya faru da Turkiyya ke ji. An kuma fada masa cewa, idan hakan ta sake faruwa to za a mayar da martani kamar yadda ake mayar wa da 'yan ta'adda. Müftüoğlu ya ce, an gayyaci mutumin ne saboda Rasha ce ke rike da yankin da aka harbo makamin.

Babban labarin jaridar Habertürk na cewa, ministan sadarwa na Turkiyya Ahmet Arslan ya ce, babu wani matakin ramuwa ga kasashen Amurka da Ingla bisa hana zuwa kasashensu da kayan lantarki daga Istanbul. Ya ce, ta'addanci, ta'addanci ne a ko'ina. Kuma ba daidai ba ne a dauki mataki a wani fiin tashi da saukar jirage ba amma kuma a ki dauka a wani. Saboda haka ne sai wasu mutanen su fara tunani akwai wata manufa a bayan yin hakan. Suna fatan babu wani abu a manufar yin hakan. Kuma za su kai matakin ga Hukumar sifirin jiragen sama ta duniya.

Babban labarin jaridar Yeni şafak na cewa, 'yan kasuwar yankin Gulf na ci gaba da sha'awar zuba jari a Turkiyya.. Akwai masu zuba jari sama da 500 daga ciki da wajen Turkiyya da ke halartar taron zuba jari na Turkiyya da kasashen Larabawa na yankin Gulf. An yi musayar ra'ayi da bayanai game da tattalin arzikin Turkiyya da na kasashen 'yan kasuwar. Mataimakin firaministan Turkiyya Mehmet Şimşek ya ce, Turkiyya na da manufofi sosai game da kasuwanci da kasashen Larabawa.

 Labarai masu alaka