Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, jiya ne aka yi bikin bude hanyar karkashin kasa na Avrasya wanda ya hada yankunan Asiya da Turai. ‘Yan ta’addda da suke kai hare-hare a cikin kwanankinan, sun hana al’umman Turkiyya walwala. Amma sai dai wannan bai hana an ci gaba da bikin bude hanyar ba. an bude wannan hanya ne karkashin ruwa na nisan mita 106 wanda ake kira da Avrasya wanda ya hada yankunan Asiya da Turai a Istanbul. Wannan aiki da mutane ke kira da yana daukar hankalin mutanen zai hada unguwannin yankin tekun Mediterenean da Marmara a birnin Istanbul. A ranar 26 ga watan Fabrairun shekarar 2018 kuma za a bude filin tashiwa da saukar jirgi mafi girma a duniya a Istanbul.

Babban labarin jaridar Habertürk na cewa, mafarki ya zama gaskiya. An kammala aikin hanyar karkashin kasa na Avarasya wanda ya hada yankuna biyu da watanni 8 kafin tarihin da aka bayar. A halin yanzu mutum zai iya anfani da mintuna 5 domin fita daga yanki daya zuwa wani yankin. Bas da kananan motoci zasu iya bin karkashin hanyar. An gina hanyar ta yadda za a kiyayeshi daga girgizar kasa. Gina wannan hanya ya sake zama sanadiyyar hada yankuna biyu. Da yake magana a taron bikin bude hanyar, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya ce, a yayin da muke yaki da ta’addanci a gefe guda kuma muna ci gaba da yin manyan ayyuka. Erdoğan ya ce, yaki da ta’addanci ba zai hana yin ayyukan kasarmu ba.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, bayan kisan gilla da aka yi wa jakadan Rasha a Ankara babban birnin kasar Turkiyya, ‘yan kasuwan Turkiyya sun la’ancin harin da aka kai. Kungiyoyin ‘yan kasuwa da dama sun fitar da sakonni inda la’anci harin da aka kai. Sun fitar da wata sanarwa da ke cewa “ba zamu yarda ‘yan ta’adda su bata dangantakar kasuwancin kasarmu da Rash aba.” Sanarwar ta kuma irin kyakyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen Turkiyya da Rasha.

Babban labarin jaridar Star na cewa, bayan harin kisan gilla da aka yi wa jakadan Rasha a Ankara babban birnin kasar Turkiyya, an gano cewa kungiyar ta’adda  ta FETÖ ke da alhakin harin kuma a baya sun yi kokarin bata dangantakar tsakanin Turkiyya da Rasha ta hanyar harbo jirgin saman Rasha. A halin yanzu an kama limamin wani masallaci a garin Izmir domin ana ganin cewa yana da alaka da wanda ya kai harin. An gano cewa a lokacin da maharin ke yake karatu a makarantar ‘yan sanda ne suka hadu da limamin inda har yanzu bai ci gaba da kulla alaka. A baya ma an kama dan’uwan limamin da zargin cewa yana da alaka da kungiyar ta’adda ta FETÖ. An kuma gano cewa ‘yan ta’addan FETÖ ne suke bashi kudade.

 Labarai masu alaka