Waka ga shahidan da suka rasa rayukansu a harin Istanbul

Waka ga shahidan da suka rasa rayukansu a harin Istanbul

Waka ga shahidan da suka rasa rayukansu a harin Istanbul

Mun binne 'yan sandanmu da yawa.

Sun bar jarirai a gidajensu wadanda ba za su san su waye iyayensu ba.

Sun bar iyayensu mata da hawayensu ba zai daina zua ba wadanda ba za su manta da kanshinsu ba.

Mun kuma binne matasanmu da yawa su ma. Ba za su ci burinsu na rayuwar duniya ba.

Muna yin addu'o'inmu tare da ajje furenni a kan kaburburansu. 

Daga nan kuma sai mu dauki dawainiyar iyayensu da 'ya'yansu mu ci gaba da tafiya tare da su.

Saboda ba ma tsoro.

Saboda mun san cewa, a wannan duniya babu wani guri, lokaci da wani zai shirya tsiya ba tare da ya fada cikinta ba.

Mu muna kara yawa a lokacinda muke samun shahidai. saboda muna zama sabbin iyaye na 'ya'yan da shahidai suka bar mana a matsayin amana.

Da haka muke kara karfi. Muna zama daya tilo.

Muna nan zuwa kanku. Za ku kare baki daya.Labarai masu alaka