Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya.

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, jiya babban hafsan sojin Turkiyya Janar Hulusi Akar ya ziyarci kasar Rasha. Akar na ziyarar kasar ne tare da sakataren Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya Hakan Fidan. A yayin ziyarar, an tattauna game da yadda za a yaki kungiyar Daesh a Siriya da kuma reshen kungiyar ta’adda ta PYD reshen kungiyar PKK da ke Siriya da kuma tura kayayyakin taimako na bil’adama a garin Aleppo. Bayan haka kuma an tattauna yadda za a dauki matakin kiyaye Mosul, da kuma iyakar Iraki da Siriya.

Babban labarin jaridar Star na cewa, a ranar 13 ga watan Nuwamban wannan shekara ne Turkiyya zata gudanar babban gasar tseren Vodafone Istanbul Maraton na karo 38. Gasar wannan shekara, za a gudanar da shi ne domin tunawa da wadanda suka yi shahada a ranar 15 ga watan Yuli. Wannan gasa da ake sa ran cewa mutane dubu 30 zasu halarci, za a ci gaba da yin rejista har zuwa 12 ga watan Nuwamba. Dukkan wanda ke son ya samu cikakkaen bayani game da wannan gasa, zai iya duba a kan shafin sada zumunci na Facebook ko kuma adreshin yanar gizo www.istanbulmarathon.org.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, bayan hukuncin da kasar Amurka ta yankewa Saudiyya game da harin da aka a ranar 11 ga watan Satumba a Amurka, masu zuba jarin kasashen yankin Gulf da suka sinci kansu cikin barazana sun yanke hukuncin aikin hadin gwiwa na kasar Turkiyya. Turkiyya ta ba yankin Gulf damar zuwa ta zuba jarin dalar Amurka Triliyon 1. Da yake bayani a taron kasuwaci da zuba jari a Bahrain, ministan kasuwanci da hana fasakori Bülent Tüfenkçi ya kirayi masu zuba jarin yankin Gulf da su zuba jari kasar Turkiyya.

Babban labarin jaridar Haberturk na cewa, wannan shi ne karo na farko da yawan masu bude ido daga kasar Rasha suka ziyarci birnin Antalya idan aka kwatanta da shekarar 2015. Alkalumman filin tashiwa da saukar jiragen Antaliya na nuna c ewa, a cikin watan Oktoba yawan masu yawon bude ido daga kasar Rasha zuwa Antaliya ya tashi zuwa dubu 129 da 539. A cikin sheakrar da ta gabata, yawan mutane da suka kai ziyara ya kai dubu 126 da 609.Labarai masu alaka