Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, kamfaninikan zuba jarin makamashi sun fara maida hankali a nahiyar Afirka domin samun ci gaba makamashin duniya baki daya. A halin yanzu, masu zuba jarin kasashen Turkiyya da kuma wakilai daga Afirka zasu halarci taron ‘Tattalin arzikin Turkiyya da Afika da kuma Aiki’ a Istanbul a tsakanin ranakun 2-3 ga watan Nuwamba karkashin jagorancin hukumar tattalin arzikin kasashen waje. Wannan taro da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai halarci, za a tattauna game da albarkatun kasa da ke nahiyar Afirka, ministoci daga kasashen Afirka daban-daban, masu zuba jari, wakilan kamfaninika, bankin Tarayyar Afirka, da kuuma sakatatorin kungiyar tattalin arzikin kasashen Afirka zasu halarci.

Babban labarin jaridar Star na cewa, shugaban kamfaninn Eesti Ernergy daga kasar Esthonia, Hando Sutter, kamafanisu kamfani mafi girma wurin samar da makamshi ta hanyar anfani da man fetur inda ya kara da cewa, “zamu yi kokarin garin cewa mun yi aikin hadin gwiwa da kasar Turkiyya domin irirn samun ci gaba da ake yi a kasar.” Ya ce, zasu iya su yi aiki da masu zuba jarin kasar Turkiyya a gundumomi kamar, Göynük da ke Bolu, Dodurga da ke Çorum, Merzifon da ke Amasya, Yozgat da ke Sorgun, tare da Tunçbilek da Seyitömer da ke Kütahya.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, sauran ‘yan kwanaki a bude masallacin Haydar Kadı da ke garin Manastir na kasar Makendonia wanda aka kama gina a lokacin daular Uthmaniyya. Tun daga shekarar 2015 ne ma’aikatar asusun kasar Turkiyya ta yi wa masallacin Haydar Kadı wanda aka gina a garin Manastir kasar Makedonia a tsakanin shekaru 1561-1562 a lokacin Kanuni Sultan Süleyman, kwaskwarima. Wannan masallaci da mutanen yankin suka yi wa suna “gimbiyar Balkas”, ya dauki tsawon shekaru 104 babu wanda ke anfani da shi. A ranar 4 ga watan Nuwamba ne ake shirin bikin bude masallacin da sallar juma’a.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, ministan al’adu da yawon bude ido Nabi Avcı ya fitar da sako mai muhimmanci game da hana tone-tonen tarihi da aka yi mayan an samu matsala tsakani kasashen Australiya da Turkiya inda ya ce, babu wani mataki na kwarai da Australia ta dauka bayan an samu matsala da su, amma sai dai a cikin ‘yan karamin lokaci wakilai zasu gana da ma’aikatar ministan harkokin waje domin tattaunawa. Avcı masu tone-tonen kasa daga kasar suna da matukan kwarewa a cikin aikin da suke yi inda ya kara da cewa, nan gaba Australia zata bukaci da masu tone-tonen su zo kasarsu domin aiki.

 Labarai masu alaka