Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, a yayin bikin cikar Jam'iyyar AKP shekaru 15 da kafuwa,shugaban kasar Turkiyya Reccep Tayyıp Erdoğan ya yi wa 'yan jam'iyyarsa jawabi ta wahar tarho.Shugaban ya ce suna ci gaba da daukar matakan da suka dace domin ganin bayan kungiyar ta'adda ta Fetullah Gulen, wadda ta yi yunkurin juyin mulki a daren 15 ga watan Yuli.Haka zalika, shugaban Turkiyyan ya ce ,kungiyar FETO ta zubar da jinin 'yan kasar Turkiyya,saboda haka sai sun ga abinda ya ture wa Buzu nadi a wajen kawon karshen ta.

Babban labarin jaridar Haber Türk na cewa, a yayin wani shirin talabijin da aka shirya a albarkacin bikin cikar jam'iyyar AKP shekaru 15 da kafuwa,firaministan kasar Turkiyya Binali Yıldırım ya yaba wa 'yan kasarsa, irin yadda suka hade kai a wajen dakile yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli.Yildrim wanda ya ce, za su ci gaba da tattalin hadinkan da Turkawa suka nuna a babban taron goyon bayan demokradiyya na Yenikapin birnin Istanbul.Daga bisani ya tabbatar da cewa ba tare da sun yi kasa a gwiwa ba, za su dunkule su zama daya da al'umarsu domin ci gaba da kare martabar kasarsu da ta demokradiyyarsu.

Babbban labarin jaridar Hürriyet na cewa, daya da cikin manya-manyan jam'ian diflomasiyyar kasar Amurka James Jeffrey ya ce, a yanzu sun gano ainahin aniyar wadanda suka yi yunkurin juyin mulki a kasar Turkiyya a ranar 15 ga watan Yuli.Munafarsu ita ce, yin watsi da mulkin demokradiyya domin kafa wani boyayyen mulkin bayan fage.Jeffrey ya ci gaba da cewa, tuni kasar Amurka wadda ta ce ba za ta mika Gulen ga kasar Turkiyya har sai an gabatar mata da kwarrarun hujjoji, ta gano gaskiyar lamarin.Domin dukkanin dalilan da ake so a yanzu,na nuna cewa 'yan kungiyar Fetullah Gulen na da hannu a yunkurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yuli.Saboda haka,lokaci ya zo da ya kamata ace an gurfanar da su a gaban kotu.Labarai masu alaka