Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, an mikawa Amurka dukkan takarduna da suke nema domin su aiko shugaban kungiyar FETO wato Fetullah Gulen zuwa Turkiyya ko da yake basa son su yi haka. Ta haka ne za a samu damar bincike akan wannan mutumin. A cikin takardunan da suka mikawa Amurka an nuna yadda wannan mutum ya zama mai cin amana, ha'intar kasa da kuma yada ya boye rayuwarsa da baya son mutane su gane. Takarda na biyar kuma na nuna yadda Gulen ya shirya yunkurin juyin mulki a kasar Turkiyya. Firaministan Turkiyya Binali Yildirim ya ce, 'Sojojin da aka kama sun fada da kansu cewa Gulen ne shugaban yunkurin juyin mulki da aka yi. shi ya sa mun yarda cewa Amurka ba zata taba barin shugaban 'yan ta'adda ya zauna a kasarsu ba."

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa Amurka ta shi ga cikin damuwa bayan da aka gano hirar da ta yi da 'yan kungiyar FETO a yunkurin juyin mulki da aka yi a ranar 15 ga watan Yuli. Shugaban jami'an tsaron kasar Amurka Joseph Dunford, da General John Campbell soja da yayi ritaya sun yi kokarin karyata labarin cewa su ne suka shirya yunkurin juyin mulkin kasar Turkiyya. Dunford yayi bayanin cewa, 'ban san inda aka samo wannan labari ba.' Kuma wannan bayaninsa ya nuna cewa yana kokarin boye wani abu.

Babban labarin jaridar Star kafin an yi yunkurin juyin mulki a kasar Turkiyya, 'yan ta'addan PKK sun shirya wani harin da zasu kai amma da ba'a yi nasarar juyin mulkin ba sai kungiyar 'yan ta'addan FETO suka sauka garin Van inda PKK suke. A halin yanzu 'yan sanda na ci gaba da bincike game da yankin domin kama mambobin FETO da PKK a garin Van. 

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, mataimakin firaministan kasar Turkiyya Mehmet Simsek ya ce, bayan al'ummar kasaar Turkiyya sun hana kungiyar ta'adda FETO juyin mulki a kasar Turkiyya, sun kuma yi nasarar hana juyin mulki a bangaren kasuwanci. Simsek ya bayyana cewa, 'yan kasar sun canca kundinsu na dalar Amurka biliyan 9 zuwa kudin Turkiyya wanda hakan na da matukan muhimmanci inda ya kara da cewa 'zamu rufe dukkan hanyoyin da aka bi domin yunkurin juyin mulki.'Labarai masu alaka