Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, a yayin da ake tattaunawa domin a samu hadin kai wurin dangantakar kasashen Turkiyya da Isra'ila, firaministan Falasdinawa da ke Gazza İsmail Haniye ya fitar da wata sanarwa inda ya ce "Turkiyya na ci gaba da gudanar da ayyukanta domin bata son ta karya alkawarinda ta yi mutanen Gazza. Turkiyya ta fi karfi akan teburun tattaunawar. Abinda ke da muhimmanci a garemu shi ne matsalar tashar jiragen ruwa. Idan aka bude jiragen ruwan to mu bamu da wata matsala a bangarenmu."

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, a cikin wasu rahotanni da aka samu daga kasashen Iraki da Siriya, 'yan ta'addan kungiyar Daesh tana yaudarar mutanen ne domin su shiga cikin kungiyarsu bayan haka kuma sai su hanasu fita. A cikin wata bayanin da shugaban kungiyar leken asirin kasar Faransa Didier Le Bret ya yi wa kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, "a halin yanzu sun fara gane cewa basu da wani iko. 'Yan ta'adda da dama na kokarin ganawa da hukumomin kasashensu domin su samar damar komawa zuwa kasashensu. Wasu da dama kuma an kashesu a lokacin da suke kokarin guduwa daga kungiyar."

Babban labarin jaridar Haberturk na cewa, shugaban kasar Amirka Barack Obama ya sake sukar dan takarar shugaban Amirka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump inda ya ce, "kamata ne a zabi shugaba wanda zai iya ya gudanar da aiki kasa sosai amma sai dai ina cikin matsala domin bani da tabbas ko wannan mutum zai iya aikin yadda ya kamata."

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, a yau za a fara gasar cin kofin Euro 2016 wanda masoyan wasanni suka dade suna jira. A cikin wata bincike da kungiyar ING Bank ta gudanar, Turkawa ne suka fi kowa kallon wannan wasanni. A yayin da kason mutane 9 daga Nahiyar Turai suka bayyana cewa zasu iya biyan fin euro 200 domin su je sukalli wasa, Turkawa kaso 23 ne suka bayyana cewa zasu iya yin hakan. Labarai masu alaka