Manyan labaran wasu daga cikin jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu daga cikin jaridun Turkiyya 07-06-2016

Manyan labaran wasu daga cikin jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar SABAH na cewa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan, ya bada sanarwar halartar makokin margayi shahararren dan wasan dambe na Amurka Muhammad Ali wanda za a gudanar a ranar Juma’a 10 ga watan Yuni. Sanarwar ta nuna cewa shugaban kasar Turkiyya zai je Amurka gobe da yamma inda zai yi ban kwana da margayi Muhammad Ali.

Babban labarin jaridar YENİ ŞAFAK na cewa shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bada sanarwar zuba jarin kudi dala biliyan 50 a nahiyar Afirka. Erdoğan ya  sanya hannun yarjejeniyar tabbatar da wannan aikace aikace ne yayin da ya kai ziyara a wasu kasashen Afirka mako da ya gabata. Ministan harkokin tattalin arzikin Turkiyya Nihat Zeybekçi ne ya bada sanarwar zuba jarin fid da kaya tsakanin bangarori biyun. Ya ce an an samu ribar biliyan 20 daga biliyan 3 da aka zuba jarri tsawon shekaru 12 inda ake yunkurin cimma burin daduwar biliyan 50. Dangane da shirye shiryen kasuwanci ne za a bude wasu bankunan Turkiyya a nahiyar Afirka don cimma wannan buri.

Babban labarin jaridar HÜRRİYET na cewa Hillary Clinton na cikin halin tsaka mai masuwa dangane da zirga zirgar yanke shawarar kasancewar wanda zai tsaya a matsayin dan takarar zaben shugaban kasar a bangaren Democrats. A gefe guda kuma jam’iyyar Republican ta zabi Donald Trump a matsayin dan takarar a zaben shugaban kasar Amurka wanda za a gudanar a ranar 8 ga watan Nuwamban bana. Hillary za ta zama mace ta farko a matsayin ‘yar takarar zaben shugaban kasar Amurka.

Babban labarin jaridar VATAN na cewa Babban bankin Amurka ya ce akwai fargaba game da fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai domin bincike da aka yi ya gano fadowar kudin Pound. Dangane da shirye shiryen gudanar da babban taro a ranar 23 ga watan Yuni ne aka fitar da wasu bincike wanda suka gano cewa makonni uku da suka gabata kudin Pound na Birtaniya ya fadi yayinda  aka kwatanta da Dalar Amurka. Wato ya fadi da kaso 1 bisa dari.Labarai masu alaka