Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya.

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Star na cewa, jiya shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya fitar da sakoni 4 a taron jami'an tsaron kasa da aka yi. Wadannan sakonni zasu za a yi anfani da shi wurin yaki da kungiyar 'yan ta'adda da ke barazana da rayuwar mutane. Dukkan dan ta'addan da ya mika kansa ga jami'an tsaro don bashi da wani hanya, ba zai iya wakiltar mutane ba. Kungiyar YPG, kungiyar 'yan ta'adda ne. Dole sai an karfafa tsaro a kowanne yanki.

Babban labarin jaridar Haberturk na cewa, jami'an tsaron kasar Turkiyya sun kaiwa 'yan ta'addan PKK faramakai a wurare fin 10 ciki har da Sur, Cizre, Yüksekova, Silopi inda suka batawa 'yan ta'addan lissafi. A cikin 'yan kwanaki biyun nan, kungiyar ta'adda ta PKK 67 ne suka gabatar da kansu ga jami'an tsaro a Mardin. Farmakin da jami'an tsaro ke kaiwa 'yan ta'adda cikin hakuri ya ragargazasu. 

Babban labarin Sabah na cewa, bayan an gama gina sabon filin tashiwa da saukar jirgin saman birnin Istanbul, zai zama mafi girman filin tashiwa da saukar jirgin sama inda masu zuba jari da dama zasu zo kasar. Kungiyar 'yan kasuwa ta Istanbul (ITO) zasu bude wani gidan kasuwanci a gefen babban filin da za a gina filin jirgin saman mai mita miliyan 76. Kungiyar sun gana da magajin Istanbul inda ya basu fili mita dubu 500 wanda zasu gina gidan kasuwanci. 

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, bangaren harkokin gine-ginen kasar Turkiyya na samar jarinsa kai sai, a hanzu ya samar da karfin da ba zai ci bashin bankin ba. Babu kamfani da ya samu ci gaba kamar bangaren gine-gine a kasar Turkiyya domin idan aka duba a cikin farkon watanni uku na wannan shekara, bangaren ta samu ci gaba da kaso 60 daga kudade lira miliyan 86 zuwa 135.  A cikin wannan shekar kuma an samu ci gaban harkan kasa da kaso 40 da kudade lira biliyan 3.Labarai masu alaka