Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya.

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, a cikin watanni 10, an yaki kungiyar ta'adda wanda suka kashe sojojin kasar Turkiyya, suka rushe gidaje, makarantu, masallatai, inda aka kashe mambobinsu da dama. A halin yanzu an kashe 'yan ta'adda dubu 2 da 172 a cikin farmakin da aka kaimusu. Kungiyar 'yan ta'addan sun fara guduwa suna barin yankin da suke. A Şirnak, an yaki 'yan ta'adda kaso 85 cikin dari. Sauran 'yan ta'addan da suka saura a yankin, an fara kamasu daya bayan daya. A gefe guda kuma ana ci gaba da bincike akan ababan fashewa da 'yan ta'addan suka binne.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa jaridar Yeni Şafak ta gano wurin da kungiyar ta'adda ta Daesh ke samar bincike, bam da kayayyakin yaki. An gano kuma yadda kungiyar ke sa 'yan kauyen Siriya aiki wurin kera makaman yaki. Wuraren da kungiyar ke kera makaman yaki su ne  El Bap, Çobanbey, Mera da kuma kauyen Able. Kusan shekara daya kenan da kungiyar Daesh ke anfani da filayen a kauyukan wanda ke girmansa ya kai eka 2. Kuma a cikin hare-haren da kawancen kasashen duniya karkashin jagorancin da kuma sojin Rasha ke kaiwa a Siriya, babu wanda ya kai hari a wurin. 

Babban labarin jaridar Hürriyet na cewa, shugaban kamfanin TAV Holding Sani Şener ya ce a cikin shekaru biyu mai zuwa zasu fara aiki a kasashe kamar Vietnam, Indonesia, Malaysia da India. Şener ya kuma kara da cewa, "A kasar Indiya kawai zamu gina sabbin filayen jiragen sama 50, kamfanin TAV ne zata bada shawarar haka yin hakan. A nahiyar Afirka kuma zamu yi aiki a kasashen da suke da masu fita kasashen waje sama da miliyan daya. Zamu kuma ga cewa mun fara aiki a yankin kasashen yankin Gulf."

Babban labarin jaridar Haberturk na cewa ana samun ci gaba a bangaren yawon bude ido a kasar Turkiyya. Ministan yawo bude da al'adun kasar Turkiyya Mahir Ünal zai ziyarci kasar Iran tare da wakilai daga kasashenJamus, Spaniya da Holland. A yayin ziyararsa Ünal zai gana da wakilai masu muhimmanci a bangaren yawon bude ido. Ana sa ran cewa kasashe biyun zasu tattauna game da yadda zusu zuba jari. A cikin shekarar 2013, 'yan yawon bude idon kasar Iran miliyan 1 da dubu 196 ne suka ziyarci kasar Turkiyya. A cikin shekarar 2014 kuma yawan 'yan yawon bude ya tashi zuwa miliyan 1 da dubu 590 inda a cikin shekarar 2015 kuma ya kusa miliyan 2. Labarai masu alaka