Manyan labaran wasu daga cikin jaridun Turkiyya

Ga manyan labarai daga wasu jarşdun Turkiyya

Manyan labaran wasu daga cikin jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hürriyet na cewa Turkiyya ta fitar da sharudda 6 ga Tarayyar Turai game da gwagwarmayar 'yan gudun hijirar Siriya.Sharadi na daya: Tarayyar ta yi gaggawa gurin janye viza wa Turkawa dake son shiga nahiyar Turai. Na biyu:Tarayyar ta kara Yuro biliyan 3 bisa kan biliyan 3 da ke nan ajiye. Na uku: A kowane dan gudun hijira da Tarayyar ta karbi dole ta taho Turkiyya ta dauki adadin da ta dauka.Wato kowane dan gudun hijira daya ya yi sanadin daukar mutun daya daga Turkiyya. Na hudu: Tarayyar ta sake bude zantuttukar amincewar Turkiyya a matsayin mamba a cikinta. Na biyar: Basussukan da zasu zo gaba Tarayyar Turai ne za ta biya, Saanan sharadi na kaarshe:Tarayyar Turai ta dauki dukkan 'Yan gudun hijira dake tsibirin Girka .

Babban labarin jaridar Habertürk na cewa Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya gana da kungiyoyin mata dake kasar ta Turkiyya a fadarsa dangane da bukukuwan ranar kare yancin mata a duniya.Erdoğan yay i Magana ya ce Turkiyya nada nata tsari da ta shirya game da kare yancin mata don haka ba dole ne ta bi dokokin Kasashen Yamma ba.Shugaba Erdoğan ya ce a tarihince ma kasar tasa ta girmama mata yadda ya kamata wanda a yankin kasashen yamma ba a gano irin haka ba.Ya ce da a ce kasashen Yamma da suka hada da Tarayyar Turai da Amurka na kaunar mata, da mata da yara kanana a Siriya basu shiga halin kaka ni ka yi ba.

Babban labarin jaridar Star na cewa dangane da bukukuwan ranar yancin mata a duniya ne matar Turkiyya suka yi kwaikwayo da 'yar kasar Iran Anousheh Ansari wadda aka sani a tarihi da nuna karfi da kwazo gurin kafa tarihin mace ta farko da ta shiga sararin samaniya karkashin hukumar NASA yayinda take da shekaru 40. Kungiyoyin mata da dama sun gudanar da bukukuwan daga murya game da kare hakkin mata.

Babban labarin jaridar Sabah kuma ta tabo yanayin duniyar kwallon kafa inda ake tattauna yiwuwar tahowar wani mai horon Turkiyya a Kungiyar kwallon kafa ta Lazio. Jaridu da dama a kasar Italiya sun ruwaito cewa akwai yiwuwar Ersun Yanal zuwa kungiyar kwallon kafa ta Lazio inda ma da kansa ya nuna kaunar hakan.Hukumar Lazi ta ce ta gana da shi Yanal sau biyu game da kwantiragin.Labarai masu alaka