Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya.

Manyan labarai daga wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Star na cewa, a cikin mako biyu ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya gana da takwaransa na Amirka John Keryy sau biyar. Cavusoglu ya bayyanawa Kerry cewa basu amince da ganawar da wakilin shugaba Obama na musamma McCurka yayi da kungiyar ta'addan PYG da kuma samun labarin cewa kungiyar ta'addan PKK sun bulla kasar Amirka. Mevlut Cavusoglu ya bada sakon cewa kamata Amirka ta nemo mafitar wannan al'smari da ke faruwa.

Babban labarin jaridar Haberturk na cewa, mataimakin shugaba mai kula da kare hakkokin bil'adam ta jam'iyyar AKP Ayhan Sefer Ustun ya bukaci da a ba garin Kilis na kasar Turkiyya lambar yabon Nobel domin wannan gari na dauke da masu neman mafakar Siriya kusa yawan adadin mutanen cikin garin. Ustun ya bayyana cewa, kasar Turkiyya misali ce ga lambar yabon zaman lafiyar Nobel domin tun daga shekarar 2011 har zuwa yanzu masu neman mafakar Siriya da ke kasar Turkiyya sun kai miliyan 3. Yawan asalin mutanen garin Kilis duu 129 ne inda yawan mtuanen Sşrşya da ke cikin garin kuma 120.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, a yayin da kasar Iran ke taimakawa Rasha tana kashe fararen hula a garin Aleppo na kasar Siriya, a gefe guda kuma Amirka da nahiyar Turai ta budewa utanen Siriya dubu 100 hanyar shiga kasar Turkiyya. A halin yanzu, an kuma fara tattauna maganar shigar masu neman m

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, a cikin 'yan shekarun nan, 'yan yawon bude idon sun fi zuwa yankin Black Sea na kasar Turkiyya. A halin yanzu 'yan yawon bude ido daga kasashen Larabawa, Gabas mai nisa da kuma nahiyar Turai suna yawan ziyarar yankin Black Sea. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bda umarni da ci gaba da gyaran yankin domin jawo hankalin 'yan yawon bude ido. A cikin gyare-gyaren da za a yi a yankin, ciki har da sabbin gidaje domin 'yan yawon bude ido.

Labarai masu alaka