'Yan ta'addar PKK sun kashe 'yan sanda a Turkiyya

'Yan sanda 3 ne suka mutu inda wasu 4 suka jikkata sakamakon hari da makaman roka da 'yan ta'addar suka kai a lardunan Diyarbakin da Şirnak na Turkiyya.

'Yan ta'addar PKK sun kashe 'yan sanda a Turkiyya

Wani bam ya fashe a gundumar Idil da ke lardin Şirnak a lokacinda motar 'yan sanda ke wucewa.

'Yan sanda 7 ne aka jikkata sakamakon tayar da bam din da 'yan ta'addan suka yi daga nesa,inda 3 daga cikinsu suka sami munanan raunuka.

Bayan kai 'yan sandan asibitin Idil, 3 dadaga cikinsu suka rasu duk da yunkurin ceton rayukansu da likitoci suka yi.

A gefe guda kuma, wasu mahara sun kai hari kan wata motar 'yan sanda a gundumar Yenişehir da ke lardin Diyarbakir.

An samu labarin cewa, ana ci gaba da arangama tsakanin jami'an tsaro da 'yan ta'adda a yankunan.Labarai masu alaka