Birnin Istanbul (5)

Masu sauraronmu barkan mu da warhaka. Barkan mu da saduwa a shirin mu da babban birnin al’adu na Istanbul. A yau zamu baku labari tarihin shaharerren wurin da mutane ke zuwa kafin su bar birnin Istanbul. Zamu baku labarin wanda ke dauke da shekaru dubu dari da dari biyar a cikin tarihin zane-zane da kuma wanda sunansa ke cikin jerin aikin gyare-gyare da aka yi a shekarar dubu biyu da goma wato Ayasofya.

251101
Birnin Istanbul (5)

Ayasofya shahararren dandalin Sultan ahmet ne, inda akwai kayayyakin tarihi mai yawa. Idan ka ziyarci ko ka zagaya a dandalin ba zai yi wuya a ce ba ka ga Ayasofya ba. Amma cikin ginin ya fi wajensa ban sha’awa; saboda kamar fada ce da kyawunta ke kama ido. Saboda haka, maimakon mutum ya tsaya a waje ya kalli Ayasofya to gwara ya shiga ya kalli cikinta. Wannan gini da ake cewa shi ne babban gini na 8 a duniya, Yau shi ne babbar coci ta hudu a duniya. Wannan coci an mai da ita masallaci a lokacin daular Usmaniyya; a shekarar dubu daya da dari tara da talatin da shida kuma sai Ataturk kuma ya mai da shi gidan adana kayan gargajiya.

Wasu masana tarihi sun ce farkon Ayasofya an gina ta ne a shekarar dari uku da ashirin da hudu lokacin sarkin sarakuna Constantine na I. A lokacin da aka yi an yi masa ginin Basilika wato katako ne aka rufe, bayan rikicin da wasu ‘yan tawaye suka yi sai ya kone. Bayan haka sai sarkin sarakuna Theodosius na II ya gina Ayasofya karo na biyu a shekarar dari hudu da goma sha biyar a matsayin gidan ibada. Wanan karo kuma ginin Basilika aka yi masa inda kuma sarkin sarakuna Justinyen wanda aka fi saninsa da suna “Nika” kuma ya yi sabon rikicin suka kona Ayasofya. Bayan wannan rikici da aka yi, sai sarkin sarakuna ya yanke shawarar cewa zai gina babbarr coci wadda ba a taba gina irinta ba, ta haka ne sai ya kira shahararrun masu gini kamar Miletos İsidoros tare da dan Tralles Anthemios suka zo suka gina Ayasofyan wacca ake gani a yau.

An fara ginin ne a filin da aka gina basilika a shekarar dari biyar da talatin da biyu, inda aka yi amfani da wasu ginshikai daga Anatolia, an yi aikin ginin da duwatsu masu launuka daban-daban ; A karkashin masu kula da ginin su dari, an yi anfani da ma’aikata guda dubu goma wurin wanda ya dauki shekaru biyar, a shekarar dari biyar da talatin da bakwai sai aka yi bikin bude cocin.

Ayasofya ce tsohuwa kuma mafi saurin kammala ginin na wata babbar coci da aka taba ginawa a duniya. Sunanta na asali Hagia Sofia. Wani mai ginin Roma ne ya gina kubbar cocin. A wannan lokaci, ana anfani ne da wani abun madauri wurin gina kubba. Duk da haka, a tarihin gine-gine wannan shi ne karo na farko da aka yi da wani abu mai kusurwa hudu wurin gina kubba.

An gina Ayasofya ne domin nuna takama da yarda. Daga baya ne aka mayar da wurin a matsayin wurin bada labarai da nuna alama. Kowa ya yarda cewa irin wannan wuri sai dai da taimakon Ubangiji ne aka iya gina shi. Ko da yake an gina Ayasofya a karni na shida a lokacin Byzantine, kuma baya ga ita ba a taba samun irin wannan gini ba, kuma har zuwa yau ba a taba samun gini mai kubba da ya tsaya har shekaru dari tara ba. Duk da haka a shekarar dari biyar da hamsin da takwas, an yi wata girgizar kasa inda ta hallaka kubban. Kubba da aka yi ta biyu ta fi girma amma sai dai kanana ne. Wannan kubba kuma an fara ta cikin sabon karni, a lokacin da aka kusa gina rabinta sai ta rushe har sau biyu. A sherar dubu daya da dari hudu da hamsin da uku da Sarkin musulman daular Uthmaniyya Fatih Sultan Mehmet ya yi nasarar mamaye garin, sai ya ceci Ayasofya inda ya mayar da ita masallaci. A karni na goma sha shida, sai aka sake alkuki da kuma rubuce-rubecen cikin ginin ta hanyar musulunci. A tsakiyar karnin goma sha tara kuma, sai mai gine-gine Fossati suka fara gyare-gyaren gini tun daga shekarar dubu daya da dari daya da da talatin har suka kawo halin da yau muke ganin Ayasofya.

A tarihin Byzantine, Ayasofya na da muhimmaci sosai. Saboda dukkan bikin sa wa sarakuna kambi da bikin nasara duka a wurin ake yi. A daya bangaren cocin ma an yi wani sassake dake tsaye tsakanin sarukuna biyu; Constantine da Justinian, a kusa da shi kuma aka ajiye Nana Mariam da Yesu akan cinyarta, a gefe kuma sai aka yi rubutu dake nuna ruwan Istanbul na zuba a Ayasofya. Saboda haka masu ziyarar wannan bangare suna ganin kyawun wurin. A nan, kowa ya shiga wannan bangare yana mamakin wurin. Saboda idan ka shiga wurin sai ka ga kamar kubban cikin iska suke kuma ka kasa mai da hankali akan ginin baki daya.

Musulmai sun dauki Ayasofya a matsayin wurin bauta mai tsabta. An kewaye ginin mihrab da zane-zanen Turkawa da Sin masu kyau. Daga cikinsu akwai rubutun wani shahararren marubucin Turkiya mai girma Kazasker Mustafa Izzet inda ya rubuta ayar Alkur’ani mai girma akan daya daga cikin kubbobin. A Ayasofya, akwai kaburburan manyan daular Usmaniyya da dama, da makarantu, da kuma misalin dakunan karatu da Turkawa ke anfani da shi a yau. Batu na gaskiya shi ne ba za a iya baka cikakkiyar labarin kyawun Ayasofya ba domin sai ka gani da kanka.

Masallacin Ayasofya na cikin jerin kayan tarihin hukumar kula da ilimin kimiyya da raya al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) masu muhimmanci, wannan shi ne ya sa a shekara ta dubu daya da dari tara da casa’in da biyu zuwa shekarar dubu daya da dari tara da casa’in da uku UNESCO suka bayar da taimako wurin gyare-gyarenta. Wannan shi ne dalilin da ya sa kubban da aka yi mai tsawon mita ashirin da shida ko ashirin, aka mai dashi zuwa tsawon mita hamsin da biyar tare da nauyin karafa dari da tamanin da daya. Wannan karafan da aka yi anfani dasu, ya gyara kubban da aka yi a shekaru goma sha shida da suka gabata. Amma a shekarar dubu biyu da goma, Ofishin ministan al’adu da kungiyar dillalan raya al’adu na shekarar dubu biyu da goma sun dauki mataki akan cewa za su gyara Ayasofya. A taron da kungiyar dillalan suka yi a ranar goma sha bakwai ga watan Janairu, sun yi bayanai game da gyare-gyaren da za su yi a wurin. Har ma sun sanar da cewa sun fara shirye-shirye. A karshen watan Yuni na wannan shekara, inda za’a kammala shirye-shiryen gyaran wurin. A halin yanzu, za’a fara gyaren da aka jima shekara da shekaru ana jira. A cikin gyare-gyaren, za a gyara dakin karatun Mahmut na I kuma za’a gyara kaburburan dake wurin; tare da lambun wurin da kuma dakin ajiye kayan al’adu. Ana sa ran cewa kafin karshen watan Nuwamba an kammala gyare-gyaren Ayasofya.

A shekarar dubu biyu da goma, babban birnin al’adun kasashen Turai ya zama babban wuri da miliyoyin mutane suka ziyarta.


Tag:

Labarai masu alaka