Türkiye ta yi magana kan zaben raba gardama na Yukren da Rasha

Türkiye ta bayyana damuwarta kan yunkurin gudanar da zaben raba gardama a wasu sassan Yukren da ke karkashin ikon Rasha.

1883096
Türkiye ta yi magana kan zaben raba gardama na Yukren da Rasha

Türkiye ta bayyana damuwarta kan yunkurin gudanar da zaben raba gardama a wasu sassan Yukren da ke karkashin ikon Rasha.

Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta fitar da wata sanarwa kan wannan batun.

A cikin sanarwar an bayyana cewa, "Mun damu da yunkurin gudanar da zaben raba gardama a wasu sassan Yukren da ke karkashin ikon Rasha. Kasashen duniya ba za su amince da irin wannan haramtacciyar hujjar ba. Sabanin haka, yin bitar tsarin diflomasiyya zai dagula kokarin da ake, ya kuma kara zurfafa rashin zaman lafiya. Muna sake jaddada goyon bayanmu don 'yancin yankin, 'yancin kai da ikon Yukren', wanda muke jaddadawa tun lokacin da aka mamaye Iraki ba bisa ka'ida ba, da kuma shirye-shiryenmu na ba da gudummawar da ta dace don warware yakin (Rasha da Yukren) da ke gudana ta hanyar yin shawarwarin lumana kan batun."

An sanar da cewa za a gudanar da zaben raba gardama daga ranakun 23 zuwa 27 ga watan Satumba akan ko yankunan Donetsk, Luhansk, Kherson da Zaporozhye na kasar Yukren za su shiga Rasha.Labarai masu alaka