Erdogan: Za a kafa asusun zuba jari na kasahen Turkawa a Istanbul

Shugaban kasar Türkiye, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa asusun zuba jari na Turkawa zai ba da gudummawa wajen hada-hadar tattalin arziki a kasashen Turkawa.

1961269
Erdogan: Za a kafa asusun zuba jari na kasahen Turkawa a Istanbul

Shugaban kasar Türkiye, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa asusun zuba jari na Turkawa zai ba da gudummawa wajen hada-hadar tattalin arziki a kasashen Turkawa.

Shugaba Erdogan ya yi bayani game da taron kolin Kungiyar kasashen Turkawa (OTS) da aka gudanar a harabar fadar shugaban kasa da ke Ankara, babban birnin kasar.

Erdogan ya bayyana cewa sun samu nasarar kammala taron. Ya ce sun gudanar da taron da mambobi da masu sa ido na kungiyar domin ba da hadin kai bayan bala'o’in girgizar kasa da ambaliyar ruwa a Türkiye.

Da yake gode wa shugabannin kasashen da suka halarci taron, Shugaba Erdogan ya ce, "Ba za mu taba mantawa da hadin kai da goyon bayan da kuka nuna ba a matsayin kasashen Turkawa yayin da muka fuskanci irin wannan bala'in."

Erdogan ya bayyana cewa burinsu shi ne gina isassun gidaje masu inganci don biyan bukatun gidaje a yankin girgizar kasar cikin shekara guda.

Erdogan ya kuma bayyana cewa sun kuma yi nazari kan hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki, kasuwanci, sufuri da makamashi, wadanda su ne injunan hada kai a duniyar Turkawa. Ya ce, sanya hannu kan yarjejeniyar kafa asusun zuba jari na kasahen Turkawa na daya daga cikin nasarorin da aka cimma. Godiya ga asusun, za a ba da tallafi ga kanana da matsakaitan masana'antu, aiyukan raya kasa, zirga-zirga da jigilar kayayyaki, aiyukan samar da ababen more rayuwa, saka hannun jari a fannin noma da yawon bude ido da nazari kan makamashi da ake iya sabuntawa."

Erdogan ya kuma jaddada cewa asusun zuba jari na kasahen Turkawa zai ba da gudummawa wajen hada-hadar tattalin arziki a kasashen Turkawa.

Ya ce, "Istanbul za ta karbi bakuncin asusun da za a kafa. Ta wannan hanyar, mun tabbatar da babban rawar da Istanbul ke takawa a fannin hada-hadar kudi ta duniya."Labarai masu alaka