Corona: An zargi wasu 'yan siyasar Faransa da karya dokar hana zirga-zirga

Wasu Ministoci da 'yan majalisar dokokin Faransa sun ziyarci gidajen sayar da abinci na boye wanda hakan ya karya dokar hana zirga-zirga da aka saka don yaki da annobar Corona (Covid-19) a kasar.

1614696

Tashar talabijin ta M6 da ke Faransa ta bayyana cewa, wasu Ministoci da 'yan majalisar dokokin Faransa sun ci abinci a gidan sayar da abinci na boye da ke Paris.

Tashar ta dauki bidiyon da ke nuna yadda ma'aikatan gidan sayar da abinci da maziyartan sa ba su saka takunkumi ba.

Haka zalika wani mutum ya shaida cewa, a makon nan wasu Ministoci da 'yan majalisar dokokin Faransa sun je tare da cin abinci a wajen.

Helkwatar 'yan sandan Paris ta bayyana fara gudanar da bincike game da lamarin.

 Labarai masu alaka