An bude mashigar teku ta Suwaish ga jiragen ruwa

Hukumar Kula da Mashigar Teku ta Suwaish ta bayyana cewa, an samu nasarar motsa jirgin ruwan dakon kaya na Ever Given da ya tsaya tare da toshe mashigar. A yanzu an bude hanyar ga jiragen ruwa na duniya.

1610932

A ranar 24 ga Maris ne jirgin ruwan dakon kaya na kasar Japan, sakamakon munin yanayi da guguwa ya daki gabar Mashigar Teku ta Suwaish mai muhimmanci a duniya inda ya karkace tare da hana jiragen ruwa giftawa.

Sakamakon yadda jirgin ruwan na 'Ever Given' ya toshe hanyar wucewa, an samu cinkoson jiragen ruwa a gabar tekun.

An bayyana samun tsaiko wajen rarraba iskar gas a duniya.

A safiyar Litinin din nan, Shugaban Kasar Masar Abdulfatah Al-Sisi ya fitar da sanarwa game da lamarin ta shafinsa na Twitter inda ya ce, duk da wahala da aka fuskanta amma an samu nasarar motsa jirgin ruwan, kuma komai ya koma daidai a mashigar teku ta Suwaish.

Sakamakon toshe hanyar da jirgin ruwan ya yi, a kowacce Masar na asarar dala miliyan 12-14 inda a duniya baki daya ake asarar dala biliyan 10.

 Labarai masu alaka