Scandinavian Airlines ya kori ma'aikata 1,593

Kamfanin jiragen sama na Scandinavian Airlines ya kori ma'aikata dubu 1,593 a Denmark.

1445675
Scandinavian Airlines ya kori ma'aikata 1,593

Kamfanin jiragen sama na Scandinavian Airlines ya kori ma'aikata dubu 1,593 a Denmark.

Sanarwar da Daraktan yada labarai na kamfanin Sille Beck-Hansen ya fitar ta ce, reshen Scandinavians na Denmark ya kori ma'aikata dubu 1,593, da suka hada da matukan jirgi 176, ma'aikatan cikin jirgi 684, leburori 586, injiniyoyi 96 da ma'aikatan gudanarwa 51.

Beck-Hansen ya ce annobar Corona ta illata kamfanin nasu sosai inda a yanzu suke gwagwarmayar kasancewa a raye.

Daraktan ya kara da cewar dole ce ta sanya kamfanin rage ma'aikata saboda matsalolin tattalin arziki, kuma yana ta shirye-shiryen korar wasu ma'aikatan a kasashen Norway da Sweden.Labarai masu alaka