Fitar da ababen hawa zuwa kasashen waje na bunkasa a Turkiyya

An sanar da cewa a cikin watanni biyar na farkon shekarar bana, cikin ababen hawa dubu 81 da dari 410 da aka kera a garin Sakarya dake Turkiyya an fitar da kaso 84.2 cikin dari zuwa kasashen waje

1444803
Fitar da ababen hawa zuwa kasashen waje na bunkasa a Turkiyya

An sanar da cewa a cikin watanni biyar na farkon shekarar bana, cikin ababen hawa dubu 81 da dari 410 da aka kera a garin Sakarya dake Turkiyya an fitar da kaso 84.2 cikin dari zuwa kasashen waje.

Daga garin an fitar da kananan motoci dubu 71 da dari 478, tireloli 44, manyan bas bas 272, tarakto dubu 9 da dari 456, a jumlace a cikin watannin biyar na farkon shekararr bana an fitar da ababben hawa dubu 81 da dari 410.

A garin Sakarya da ake kera kaso 19.1 cikin darin motocin da ake yi a kasar; daga cikin ababen hawa 535 da ake kerawa a rana ana fitar da 451 zuwa kasashen waje.

 Labarai masu alaka