A bana jiragen kasa masu aiki da lantarki kirar Turkiyya za su fara zirga-zirga

Ministan Sufuri da Gina Kasa na Turkiyya Adil karaismailoglu ya bayyana cewar a wannan shekarar ta 2020 jiragen kasa kirar Turkiyya masu aiki da lantarki dari bisa dari za su fara aiki.

1445554
A bana jiragen kasa masu aiki da lantarki kirar Turkiyya za su fara zirga-zirga
milli tren 2.jpg
yerli ve milli elektrikli tren.jpeg

Ministan Sufuri da Gina Kasa na Turkiyya Adil karaismailoglu ya bayyana cewar a wannan shekarar ta 2020 jiragen kasa kirar Turkiyya masu aiki da lantarki dari bisa dari za su fara aiki.

A jawabin da Karaismailoglu ya yi a wajen gwajin jirgin kasa mai aiki da lantarki a Sakarya ya bayyana cewar suna ci gaba da kirkirar kayan fasa na harkokin sufuri.

Ya ce "Manufarmu ita ce Turkiyya ta zama babbar cibiyar samar da jiragen kasa masu aiki da lantarki."

Ministan ya kuma ce jirhiinnkasan zai yi gudun kilomita 160 a awa 1, wanda an kuma samar da tsai mai kyau da zai gamsar da jama'a.

Ya kara da cewar jirgin zai dibi mutane 325 a lokaci guda kuma daga cikin kujerun cikin tarago 5 da yake da su akwai kujerun nakasassu.

Haka zalika ya kuma fadi cewar kaso 80 na kayan da aka samar da jirgin da su a Turkiyya aka kirkire su.Labarai masu alaka