Turkish Airlines ya sake kara wa'adin dawo da fara zirga-zirga a ciki da wajen Turkiyya

Sakamakon annobar Corona (Covid-19) kamfanin jiragen saman Turkiyya na Turkish Airlines ya sanar da dage lokacin dawo da fara zirga-zirga a cikin Turkiyya zuwa 4 ga Yuni da wajen kasar zuwa 10 ga Yuni.

1420969

Sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce an sake daukar matakan dakatar da zirga-zirga a ciki da wajen Turkiyya saboda barazanar da Covid-19 ke yi.

Sanarwar ta ce a ranar 4 ga Yuni za a dawo da zirga-zirga a cikin Turkiyya inda za a dawo da fita wajen kasar a ranar 10 ga Yuni.

A karkashin sabbin matakan da aka dauka, matafiya sun daina shiga cikin jirgi da jakunkuna, za a dinga saka su a karkashin jirgin.

Kuma kilo 8 na jakar hannu da mutum yake da ita za a kara shi ga nauyin babbar jakarsa.Labarai masu alaka