Mesut Ozil ya rabawa iyalai 280 kayan abinci a Turkiyya

Shahararen dan wasan kwallon kafa Mesut Ozil ya rabawa iyalai 280 kayan abinci a yankin Manisa da ke Turkiyya.

1419338
Mesut Ozil ya rabawa iyalai 280 kayan abinci a Turkiyya

Shahararen dan wasan kwallon kafa Mesut Ozil ya rabawa iyalai 280 kayan abinci a yankin Manisa da ke Turkiyya.

An bayar da kayan abincin ta hannun Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent da ke Turkiyya.

Dan wasa Mesut Ozil dan asalin Turkiyya da ke taka leda a kungiyar Arsenal ta kasar Ingila, ya bayar da gudunmowa ga gangamin neman taimakon da Kungiyar Red Crescent ta fara.

An raba kwalayen abincin da Ozil ya bayar da kudi a aka saya ga iyalai 280 mabukata a gundumomin Soma da Yunusemre da ke Manisa.

A jikin kwalayen kayan taimakon an rubuta "Tare da so da Kauna daga Mesut Ozil".

Shugaban Kungiyar a gundumar Yunusemre Serdar Sevim ya mika godiyarsu ga Mesut Ozil bisa wannan taimako da ya bayar.Labarai masu alaka