Tarayyar Turai ta amince da ware Euro tiriliyon 2 don kubutar da tattalin arziki

Majalisar Tarayyar Turai (AP) ta yi kira da ware Euro tiriliyon biyu domin kubuta daga matsalolin tattalin arziki da sabuwar kwayar cutar corona ta haifar

1418406
Tarayyar Turai ta amince da ware Euro tiriliyon 2 don kubutar da tattalin arziki

Majalisar Tarayyar Turai (AP) ta yi kira da ware Euro tiriliyon biyu domin kubuta daga matsalolin tattalin arziki da sabuwar kwayar cutar corona ta haifar.

A yayin babban taron majalisar a Brussels, babban birnin Belgium ne tsarin amincewa da kasafin kudin tarayyar da kuma ware kudaden kubutar da tattalin arziki daga matsalolin da covid-19 ya haifara ya samu amincewa da kuri'a 505.

A taron an amince da cewa akwai bukatar Euro tiriliyon 2 domin kubutar da tattalin arzikin kasashen nahiyar 27 daga matsalolin da suka fuskanta daga coronavirus.

Haka kuma an amince akan kudin da za'a ayyanar da kasafin kudin tarayyar da asusun ceton su kasance daga ma'ajiyar tarayyar a maimakon gudunmowa daga kasashen.

Matakan da basu dogara akan doka ba ana amincewa dasu ne idan majalisar da mamabobin tarayyar suka amince da ita.

 Labarai masu alaka