Turkiyya ta sake aikewa da kayan taimako zuwa Somaliya

Kakakin Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya bayyana cewar kasarsa ta sake aikewa da kayan taimako zuwa Somaliya.

1408881
Turkiyya ta sake aikewa da kayan taimako zuwa Somaliya

Kakakin Fadar Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim Kalin ya bayyana cewar kasarsa ta sake aikewa da kayan taimako zuwa Somaliya.

Sanarwar da Kalin ya fitar ta shafinsa na Twitter ta ce tun shekarar 2011 dubunnunan mutane suka rasa rayukansu a Somaliya saboda halin da kasar ke ciki, kuma a wannan wata na Ramadhan Mai Albarka sun sake aikawa da kayan agaji zuwa kasar.

Ya ce ziyarar da Shugaba Erdogan ya kai kasar a karon farko ta zama farin ciki da fata nagari a zukatan jama'ar Somaliya.

Kwanaki 2 da suka gabata Turkiyya ta aike da kayan taimako zuwa Somaliya.Labarai masu alaka