Turkiyya ta zama cibiyar samarwa da sarrafa Mujauharai a duniya

Ko kun san cewa Turkiyya ce kasa ta 5 a duniya dake sarrafa Mujauhari kuma ta 3 wajen samar da shi?

1393845
Turkiyya ta zama cibiyar samarwa da sarrafa Mujauharai a duniya

Turkiyya na daya daga cikin kasashen duniya 3 dke samar da Mujauharin zinariya, kuma tana ci gaba da nuna bambanci da yin fice saboda irin kayan ado na zamani da take samarwa da mujauharan. Saboda Turkiyya kowacce shekara tana sarrafa tan 400 na zinariya da tan 200 na azurfa ya sanya ta ta zama daya daga cikin kasashen duniya 5 da suka hada da Indiya, Rasha, China da Amurka. A wajen samar da mujauharai kuma tana cikin kasashe 3 da ita, Indiya da Italiya.

Mafi yawan shagunan samar da mujauharai suna Istanbul, sannan a Ankara da Izmir ma ana samar da su da dama. A kasuwar Kapalicarsi da ta zama cibiyar sayar da mujauharai a Istanbul akwai masu samar da su da tsara su ba ma masu daukar horon samar da su. Kapalicarsi na ci gaba da jagorantar duniya a bangaren zayyanar kayan adon zinariya, azurfa da lu’u-lu’u.Labarai masu alaka