Corona: Turkiyya ta aike da kayan taimako ga kasashen Balkan

Turkiyya ta aike da kayan taimako na kula da lafiya zuwa ga kasashen Balkan.

1393755
Corona: Turkiyya ta aike da kayan taimako ga kasashen Balkan

Turkiyya ta aike da kayan taimako na kula da lafiya zuwa ga kasashen Balkan.

Gwamnatin Turkiyya ta aike da kayayyakin zuwaga kasashen Makedoniya ta Arewa, Montenegro, Sabiya, Bosniya da Kosovo.

Jirgin daukar kaya na sojoji ne ya tashi dauke da kayan daga filin tashida saukar jiragen sama na sojoji dake yankin Etimesgut dake Ankara zuwa kasashen.

An samu labarin cewar Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne ya bayar da umarnin a aike da kayant taimakon zuwa kasashen.

Ma'aikatar Lafiya ta Turkiyya ta shirya kayan da suka hada da abubuwan rufe baki, rigunan ma'aikata da kayan gwaji da gano cutar Corona cikin sauri.

A kwanakin baya ma, a wannan lokaci da duniya take yaki da annobar Corona (Covid-19), Turkiyya ta mika hannayenta na karamci ga kasashen Spaniya da Italiya da cutar Corona ta fi addaba kuma suka zamo cibiyar yaduwar ta a nahiyar Turai.

A helkwatar Hukumar Samar da Kayan Sojoji dake karkashin Ma'aikatar Tsaron Turkiyya an dorawa jirgin sama dubunannan rigunan kariya, abubuwan rufe fuska, magunguna, sinadaran wanke hannu da sauransu inda suka tashi zuwa kasashen Spaniya da Italiya.

A jikin kwalayen da aka zuba kayan taimakon an rubuta kalaman Mevlana a yarukan Italiyanci da Spaniyanci na cewa "Bayan bakin ciki akwai farin ciki. Bayan duhu akwai hasken rana da yawa."

Haka zalika an rubuta "Soyayya daga Turkiyya zuwa ga jama'ar Spaniya."

Jirgin saman da ya debi kayan ya tashi daga Ankara inda zai fara sauka a Spaniya, sannan ya wuce zuwa Italiya.Labarai masu alaka