Mummunar ambaliyar ruwa a Indonesiya

Sama da mutane dubu dari ne suka illatu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihar West Jaba ta kasar Indonesiya.

1389737
Mummunar ambaliyar ruwa a Indonesiya

Sama da mutane dubu dari ne suka illatu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihar West Jaba ta kasar Indonesiya.

Tun ranar Lahadin da ta gabata ake ruwan sama mai karfi a Bandung Babban Birnin jihar wanda ya janyo ambaliyar ruwa a yankuna 7.

An bayyana cewar ambaliyar ruwa ta shafi mutane dubu 101,644 kuma an kwashe mutane dubu 3,298 da gidajensu suka rushe.

A daren sabuwar shekarar nan sama da mutane 60 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a Jakarta Babban Birnin Indonesiya, garuruwan Depok, Bekasi da Tangerang, yankunan Bogor da Lebak.

Mamakon ruwan saman da aka samu ne ya janyo ambaliyar ruwan.Labarai masu alaka