Lewandowski ya bayar da taimakon Yuro miliyan 1 don yaki da Corona

Dan wasan kwallon kafa dan kasar Polan dake taka leda a kungiyar Bayern Munich ta Jamus Robert Lewandowski ya bayar da kyautar Yuro miliyan 1 don yaki da cutar Corona Covid-19.

1383109

Lewandowski ya zanta da 'yan jairdu a Jamus bayan ya bayar da  taimakon tare da hadin gwiwar matarsa ya ce "Mun ankare da mummunan halin da aka shiga. Dukkanmu a sahu daya muke gwagwarmaya. Dole ne mu yi karfi a wannan yakin. Muna jiran ganin kowa ya bayar da taimako wajen yaki da cutar."

Lewandowski ya bayar da taimakon ga asusun da abokansa wasansa na Bayern Munich, Jamusawa Leon Goretzka da Joshua Kimmich suka kafa da sunan 'Muna kutufar Corona'.

Dan wasan Manchester City dan kasar Jamus Leroy Sane ma ya bayar da taimako ga asusun.Labarai masu alaka