Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 7 a Iran

Mutane 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a jihohin Iran 7.

1383551
Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 7 a Iran

Mutane 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a jihohin Iran 7.

Kamfanin dillancin labarai na Fars ya rawaito kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa Mujtaba Halidi na cewa "Sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu mutane 7 sun mutu yayinda wasu 9 suka jikkata a jihohin Hurmuzgan, Bushehir, Fars, Sistan-Balujistan, Kum, Giylan da Kirman."

Halidi ya kuma ce a gundumar Rdan ta jihar Hurmuzgan mutane 2 sun bata.

A sanarwar da kakakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawar Halidi ya fitar a ranar Lahadin nan ya ce mutane 3 ne suka mutu amma a yanzu sun karu zuwa 7.

 Labarai masu alaka