Turkiyya ta kai karar Tarayyar Turai a Hukumar WTO

Turkiyya ta kalubalanci Tarayyar Turai akan sakawa kayyayakin karafar da take fitarwa zuwa nahiyar haraji a Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO)

1382518
Turkiyya ta kai karar Tarayyar Turai a Hukumar WTO

Turkiyya ta kalubalanci Tarayyar Turai akan sakawa kayyayakin karafar da take fitarwa zuwa nahiyar haraji a Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO).

Tarayyar Turai ta gudanar da wasu bincike a watan Yulin shekarar 2018 inda ta saka wasu ka’idoji akan kayayyakin karafa da take shigowa dasu domin mayar da martani akan harajin da Amurka ta sakawa karafar da ake shigowa dasu kasarta.

A watan Febrairun shekarar 2019 ne hukumar Tarayyar Turai ta bayyana saka wasu ka’idojin kariya akan kayayyakin karafar da ake shigowa dasu domin yawan karafar da ake shigowa dasu nahiyar sun kasance kalubale ga mambobin nahiyar masu sarrafa karafa.

Tarayyar Turai ta kaiyade yawan karafa da za’a iya shiga dasu nahiyar tare da sanya harajin har kaso 25 cikin dari har na tsawon shekaru uku idan aka wuce adadin da ta kaiyade.

A matsayarta na daya daga cikin kasashen dake shiga da karafa a nahiyar Turkiyya ta kalubalnci wadannan matakan a  bangarori 17.

Ministan kasuwanci na kasar Turkiyya ya bayyana cewa matakin na nahiyar Turai ya taba harkokin fitar da bakaken karfe daga kasar, lamarin da ya sanya Turkiyya kai karar nahiyar a Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO.

 Dangane ga alkaluman da aka fitar a watan Janairun shekarar 2020 Kungiyar Karafa ta Duniya ta bayyana cewa Turkiyuya ce ta 7 daga cikin kasashe masu fitar da bakin karfe a duniya.

A shekarar 2019 Turkiyya ta fitar da bakin karfe har na dala miliyan 33.7.

 

 

 Labarai masu alaka